Turkiya ta bukaci Girka da ta daina muzgunawa Limaman Musulman Yammacin Trakya

Turkiyya ta bukaci Girka ta kawo karshen mummunar halayyar da ake nuna wa Malaman da aka tura wa Turkawa kuma Musulman Yammacin Trakya marasa rinjaye.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Hami Aksoy ya ce, an bayyana musu irin damuwar da Turkawa Musulman Yammacin Trakya marasa rinjaye suke da ita.

Ya ce, suna kira da a kawo karshen wannan mummunar dabi'a da ake nuna wa Musulmai Turkawa marasa rinjaye na Yammacin Trakya kuma a gyare-gyare da za a yi za a yi su ta hanyar biyan bukatar jama'ar yankin. Labarai masu alaka