Obama: Trump ya zama gagarabadan shugaba

Obama wanda ya share lokacin mai tsawon gaske yana zuba na mujiya ba tare da ya ce uffan ba kan siyasar kasar Amurka,ya yanke shawarar fasa tsuke baki.

Obama: Trump ya zama gagarabadan shugaba

Obama wanda ya share lokacin mai tsawon gaske yana zuba na mujiya ba tare da ya ce uffan ba kan siyasar kasar Amurka,ya yanke shawarar fasa tsuke baki.

Tsohon shugaban kasar na Amurka ya yi tsokaci a wani taro mai taken "Yanayin da Demokradiyya ta kasance a ciki a yau" wanda jami'ar Illinois ta shirya,inda ya ce

"Ababen da ke afkuwa a lokacin mulkin Trump ba daidai ba ne.Ko da yake dukannin wannan lamurran ba su fara afkuwa a zamaninsa ba.Shi ba musababbi ne, sakamako ne.Donald Trump ya zama gagarabadan shugaba.Saboda yana samun ilhama ne daga kulle-kullen da 'yan siyasar kasar Amurka suka dinka yi tsawon shekaru da dama"Labarai masu alaka