Amurka na yunƙurin kifar da gwamnatin Venezuela

An bayyana cewar gwamnatin Amurka da haddin kan wasu sojoji ƙasar Venezuela na shirys kifar da gwamnatin Venezuela a asirce.

Amurka na yunƙurin kifar da gwamnatin Venezuela

An bayyana cewar gwamnatin Amurka da haddin kan wasu sojoji ƙasar Venezuela na shirys kifar da gwamnatin Venezuela a asirce.

Jaridar New York Times (NYT) ta rawaito cewa tsohon komandan sojojin Venezuela ya bayyana cewar wasu sojojin Amurka suna tattaunawa a asirce da wasu sojojin Venezuelan a yunkurin Donald Trump na kifar da gwamnatin ƙasar.

Tsohon kwamandan ya ƙara da cewa Venezuela dake cikin jerin kasashen da Amurka ta kakkaɓawa takunkumi na fuskantar shirin kifar da gwamnatin ƙasar daga Amurka.

Ya ƙara da cewa ganin yadda yunkurin kifar da gwamnatin Venezuelan da wuya ya yi nasarar ya sanya dakatar da yunkurin.

A yayinda jami'an fadar White House suka ki amsa tambayoyi akan lamarin ministan harkokin wajen Amurka na jaddada kara kakkaɓawa gwamnatin Nicolas Maduro takunkumi.

Gwamnatin Trump ya zargi tabka maguɗi a zaben Venezuelan da aka gudanar 20 ga watan Mayis wanda Maduro ya lashe a turmin farko lamarin da ya sanya Amurka fara kakkaɓawa kasar takunkumi.

 Labarai masu alaka