Sanarwar bayan Babban Taron Turkiyya, Rasha da Iran kan Siriya

Kasashen Turkiyya, Rasha da Iran sun gana yau da nufin nemo bakin zaren warware rikicin Siriya.

Sanarwar bayan Babban Taron Turkiyya, Rasha da Iran kan Siriya

Kasashen Turkiyya, Rasha da Iran sun gana yau da nufin nemo bakin zaren warware rikicin Siriya.

A Tehran Babban Birnin Iran Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Iran Hassan Ruhani sun gana tare da tattauna hanyoyin kawo karshen rikicin inda aka kuma fitar da sanarwar bayan Taron karkashin maddodi 12 kamar haka: 

1. Tun daga watan Janairun 2017 da aka fara aiki da yarjejeniyar Astana zuwa yau, an samu raguwar rikici a fadin Siriya baki daya. An dan samu kwanciyar hankali a saboda haka kasashen sun nuna gamsuwarsu.

2. An kuma amince da cewar, dole kowanne bangare ya nuna girmama wa ga 'yanci, dama da dayantakar kasar Siriya baki daya duba da dokokin Majalisar Dinkin Duniya. An sake jaddada cewa, ba tare da kallon kowa ba, dole ne kowanne bangare ya kare wannan matsayi. An yi watsi da duk waani yunkuri na amfani da yak da ta'addanci wajen janyo rikici. An kuma bayyana hade kai don magance 'yan aware da ke Siriya wadanda ke san raunata tsaron kasashe makota.

3. An sake tattauna batutuwan da suke kasa. An duba batutuwan da aka tattauna a ranar 4 ga Afrilun 2018 a taron karshe da aka yi a Ankara kan Siriya. An kuma amince kan bangarorinn 3 za su ci gaba da aiki tare. Sun kuma amince da za a ci gaba da ganin Idl,b a matsayin yank, na rage rikici wanda ya ke karkashin yarjejeniyar Astana da aka cimma a baya. 

4. Kungiyoyin ta'adda da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ayyana su a matsayin 'yan ta'addar da suka hada da Daesh, Al-Nusra, da Alka'eda da duka wasu masu alaka Daesh, za a kakkabe su ta hanyar hada kai. A karkashin yaki da ta'addanci. An kuma nuna muhimmancin bukatar bambance kungiyoyin da suke dauke da makamai wadanda za su bi sahun gwamnati don tsagaita wuta zai taimaka wajen tsare fararen hula.

5. An sake jaddada cewar amfanida karfin soji ba zai kawo karshen rikicin Siriya ba, hanyar siyasa ce kadai za ta warware wannan balahira. An amince da ci gaba da aiki tare da abubuwan da aka cimma a taron Sochi na Rasha kan Sulhun Kasa da kuma sashe na 2254 na dokokin majalisar Dinkin Duniya.

6. An sake jaddada za a ci gaba da neman hanyar warware rikicin Siriya tare da Siriyawa kuma ta hanyar siyasa. An kuma karfafa kafa kwamitin kundin tsarin mulki da aiki da shi wanda zai taimaka wajen warware rikicin. Sun kuma nuna gamsuwa game da tattaunawar Manyan Ma'aikatan gwamnati da Wakilin Musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan Siriya.

7. An karfafa wajabcn bayar da goyon baya wajen dawo da rayuwa mai kyau da zaman lafiyar Siriyawa ta hanyar rage radadin rikicin da ake yi. Akarkashin haka an amince da aika karin kayan taimako,  saukaka hanyoyin kwance bama-bamai da aka binne, dawo da kayan more rayuwa yadda suke a baya, tare da kare kayayyakin tarihi. An kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyoyin Taimako na Kasa da Kasa kan su kara yawan taimakon da ake ba wa Siriya. 

8. An sake jaddada bukatar saukaka hanyar isa da dukkan kayan taimako ga Siriyawa da suke cikin halin bukata, kare lafiya da dukiyoyin fararen hula da kyautata ytanayinsu.

9. An kuma nuna bukatar a dauki matakan da wo da wadanda suka bar matsugunansu suka gudu wasu yankunan kasa ko sukatafikasashen waje. a karkashin wannan an nuna bukatar hadin kai tsakanin Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da sauran Kungiyoyin Kasa da Kasa da Kwararru. (SUn amince da yin wani babban taro na kasa da kasa kan 'yan gudun hijirar Siriya).

10. Sun nuna gamsuwa game da aiyukan karbo mutane, kubutar da su, mika wadanda suka mutu ga 'yan uwansu da Kwararrun Majalisar Dinkin Duniya da na Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross suka yi.

11. An dauki matakin yin taro na gaba a Rasha sakamakon gayyatar da Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya bayar.

12. Shugabannin Rasha da Turkiyya sun mika godiyarsu ga Shugaban Kasar Iran Hassan Ruhani da ya karbi bakuncin taron a Tehran. Labarai masu alaka