Alakar Turkiyya da Rasha ta shiga sabon shafi

Turkiyya da Rasha sun sake gyara dangantakar dake tsakaninsu tun bayan rikicin fadar da jirgin Rasha a shekarar 2015. Sun dauki matakan gyara dangantakarsu a fannonin siyasa, diflomasi, soja da tattalin arziki cikin gaggawa.

Alakar Turkiyya da Rasha ta shiga sabon shafi

Turkiyya da Rasha sun sake gyara dangantakar dake tsakaninsu tun bayan rikicin fadar da jirgin Rasha a shekarar 2015. Sun dauki matakan gyara dangantakarsu a fannonin siyasa, diflomasi, soja da tattalin arziki cikin gaggawa. Ƙasashen biyu sun daura ɗamarar inganta harkokinsu ta hanyar ƙaddamar da aiki bai ɗaya da yawan musayar bayanai tsakanin shugabanninsu musamman yadda matakan da Amurka ke ɗauka a ƴan kwanakin nan bai musu daɗi ba. Sai dai duk yadda ƙasashen biyu suka kusanci juna, suna da bambancin ra'ayi a fannoni da dama.

Shugaban ƙasar Rasha Putin ya bayyana aniyar ƙara inganta dangantakar ƙasarsa da Turkiyya, inda ya bayyana cewar “muna mai matuƙar buƙatar inganta dangantakar dake tsakaninmu da Turkiyya domin hakan nada muhimmanci gare mu” Kalaman shugaba Putin na karantar da irin niyyar inganta harkokin kasashen biyu, musamman a fannonin makamashi da tattalin arziki. Tsohon ministan tattalin arzikin Rasha Zadornov ya bayyana cewar “ muna da hurɗar tattalin arziki mai ƙarfi tare da Turkiyya” Turkiyya na ɗaya daga cikin ƙasashe goma da muka fi gudanar da kasuwanci dasu inji ministan. Hukumar harajin ƙasar Rasha ta bayyana cewar watanni shida farkon wannan shekarar Turkiyya ta bunkasa kasuwancinta da kaso 37 cikin ɗari da zunzurutun kudi dala biliyan 13.3 hakan ya sanya ta kasance ƙasa ta huɗu da tafi kasuwanci da Rasha a duniya. Haka kuma, yawan ƴan gudun hijirar dake zuwa Turkiyya daga Rasha ya ƙara danƙon zumuncin ƙasashen biyu. Ministan harkokin wajen Turkiyya Çavuşoğlu ya jaddada fa'ida ga yadda ƴan yawon bude ido daga Rasha ke ƙaruwa, lamarin da ya kira abin farin ciki, domin a wannan shekarar ƴan yawon buɗe ido daga Rasha miliyan 6 suka zo ƙasar Turkiyya.

A fannin makamashi kuwa, aiyukan cibiyoyin makamashin Akkuyu da bututun iskar gas da ƙasashen biyu ke gudanarwa bai ɗaya nada muhimmanci sosai akan dangantakar kasashen biyu. Cibiyar nukiliyar Akkuyu zata samar da kashi goma na makamashin da Turkiyya ke bukata lamarin da zai ƙara ingancin tattlin arzikin ƙasar. Haka kuma aiyukan bututun iskar gas nada nasa rawar dayake takawa a fagen bunƙasar tattalin arzikin kasar. Aikin bututun iskar gas ɓangare na biyu da zai kai yankin kasashen Balkan zai sanya Turkiyya a matsayar ƙasar da zata kasance wata gadar samar da gas ga yankunan.

Baya ga hurɗar tattalin arziki da makamashi, akwai ƙaruwar haɗakar soja tsakanin Turkiyya da Rasha. Musamman sayar makamin S-400 da Turkiyya tayi daga Rasha wanda za'a miƙamata a shekarar 2019 ya kasance wani lamari da ke ƙara danƙon zumuncin ƙasashen biyu. Akan hakan ne daraktan kanfanin tsaron Rasha wato Rosteh mai suna Viktor Kladov ya bayyana cewar sayar da makamin S-400 lamari ne da zai bunƙasa hurɗa tsakanin mu da sauran ƙasashen yankinmu

Bunƙasar dangantakar Rasha da Turkiyya ya kasance lamarin da ya ke cimma Amurka tuwo a kwarya. Akan hakan ne kanfunan tsaron Amurka suka yi wata barazanar dakatar da sayarwa Turkiyya da jirgin yaƙi kirar F-35. Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya bayyana cewar sayar makami kirar S-400 ba wai zaɓin Turkiyya bane kawai lamari ne daya zama dole, sabili da duk da buƙatar da Turkiyya ta yi ƙasashen NATO sunƙi sayar mata da makaman da take buƙata. Haka kuma lamurkan kungiyoyin ta'addanci FETO, PKK-YPG da kuma lamarin Brunson sun sanya tsamin dangantakar Turkiyya da Amurka wadanda dukkanninsu mambobin ƙungiyar NATO ne. Bugu da ƙari takunkumi da shugaban Amurka Donald Trump ya kakkaɓawa Turkiyya ya ƙara yan bayan dangantakar kasashen biyu. Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu a yayinda yake jawabi a Moscow babban birnin Rasha ya nanata cewa bunƙasar dangantakar Turkiyya da Rasha na ƙara sanya wasu ƙasashe kishi.

Koda yake duk da bunƙasar dangantakar dake tsakanin Rasha da Turkiyya, a wasu fannonin suna da bambancin ra'ayi. Duk da kasashen biyu sun aminta akan yarjejeniyar Astana sun yiwa juna hannun riga a fagen gudanar da yarjejeniyar. Rasha ta kasance tana goyon bayan gwamnatin Siriya wajen kai hari a yankunan ldlib lamarin da Turkiyya ke ganin ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Haka kuma, Turkiyya ta ƙalubalanci Rasha a lamurkan Crimea musamman yadda take tozartawa Turkawan yankin. Bugu da ƙari, Turkiyya da Yukiren sun gudanar da yarjejeniya a fannoni daban daban musamman a fannin tsaro, wannan mataki ne dake nuna ƙalubalantar Rasha game da matakinta a Yukiren. A ƙarshe dai, duk irin yarjeniyoyi da hurɗar da Turkiyya zata ƙulla da Rasha, tana nan a matsayinta na ɗaya daga cikin ƙasashen NATO.Labarai masu alaka