Shugaban Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ya ce ba zai sake tsaya wa takara ba

Shugaban Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Joseph Kabila ya bayyana cewa, ba zai sake tsaya wa takara a zaben da aka jinkirta yin sa ba.

Jita-jitar da aka dinga yada wa cewa zai sake takara ts anya jama'a gudamnar da zanga-zanga a sasan kasar daban-daban.

A shekarar 2001 ne Kabila ya zama Shugaban Kasa bayan mutuwar mahaifinsa Laurent Kabila inda ya yi mulki zango 2. Kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ya bayar da dama a y shugabanci zango 2 ne kawai amma an dinga yada jita-jitar Kabila zai nemi zango na 3.

Wani babban jami'in gwamnatin hadin kan kasar ya tabbatar da cewa, Kabila zai sake tsaya wa takara ba.

Ya ce, sun zabi su tsayar da Emmanuel Ramazani Shadary a matsayin dan takarar gwamnati wanda zai fafata da tsohon Mataimakin Shugaban kasar Jean-Pierre Bemba Gombo.

Tun shekarar 2016 ya kamata a ce Kabila ya sauka daga mulki mma ya ki sauka inda ya dinga cewa, da yawa daga cikin masu jefa kuri'a ba su samu damar yin rejista ba.Labarai masu alaka