Ahmadinejad ya bukaci Ruhani da ya yi murabus

Tsohon Shugaban Kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewa, al'Umar Kasar ba su amince da gwamnati mai ci ba a saboda haka yana kira ga Shugaban Kasarsu Hassan Ruhani da ya yi murabus.

Ahmadinejad ya bukaci Ruhani da ya yi murabus

Tsohon Shugaban Kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewa, al'umar Kasar ba su amince da gwamnati mai ci ba a saboda haka yana kira ga Shugaban Kasarsu Hassan Ruhani da ya yi murabus.

A wani sako mai hoto da Ahmadinejad ya fitar ta shafin sada zumunta ya ce, al'umar Iran sun damu matuka da halin da ake ciki a yanzu.

Ya ce "Amincewar da al'uma ta yi wa gwamnati ta dawo matakin sifiri."

Ahmedinejad ya kare fadinsa na cewa tun bayan zuwa Ruhani da tawagarsa kan mulki jama'ar Iran suka fara cutuwa inda ya ce, hanya daya da zai samu gamsuwar jama'a shi ne kar ya ci gaba da mulki.Labarai masu alaka