Nuna wariya a Amurka ya karu bayan zabar Donald Trump a 2016

Wani bincike da aka gudanar ya bayyana cewa, daga lokacin da aka zabi Donald Trump a matsayin Shugaban Kasar Amurka nuna wariya ya karu a kasar sosai.

Kamfanin Morning Consult da ke gudanar da bincike kan sha'anin siyasa ya bayyana cewa, kaso 55 na wadanda suka amsa tambayar binciken da suka yi sun ce, yawan nuna wariya ya karu sosai a Amurka tun bayan da Trump ya hau kan mulki.

Kaso 51 na farar fata da suka amsa tambayoyin sun ce, alakarsu da sauran al'umu ta munana inda a tsakaninsu da bakaken fata 'yan asalin Afirka ta munana da kaso 79 sai da 'yan asalin Latin Amurka da ta munana da kaso 60.

A binciken da aka yi irin wannan a lokacin mulkin Obama an samukarin nuna wariya da kaso 37 inda a lokacin mulkin George W. Bush ama samu da kaso 16.Labarai masu alaka