Trump: Hadin kan Amurka da Rasha ya kubutar da rayukan dubunnan daruruwan Siriyawa

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, hadin kan da suka yi da Rasha ya kubutar da rayukan dubunnan daruruwan Siriyawa a mummunan rikicin da ake a Kasarsu.

Trump: Hadin kan Amurka da Rasha ya kubutar da rayukan dubunnan daruruwan Siriyawa

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, hadin kan da suka yi da Rasha ya kubutar da rayukan dubunnan daruruwan Siriyawa a mummunan rikicin da ake a Kasarsu.

Bayan ganawar Trump da Shugaba Putin a Helsinki Babban Birnin kasar Finland sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa.

A jawabin da Trump ya yi a wajen ya ce, hadin kan da ya kamata Rasha da Amurka su yi, zai amfani Kasashen 2 da ma duniya baki daya.

Trump ya kara da cewa, a baya alakar Amurka da Rasha ta munana fiye da kowanne lokaci amma kuma lamarin ya sauya cikin 'yan awanni kadan.

Shugaban na Amurka ya kuma tabbatar da cewa, a nan gaba za su gana da Putin sosai kuma ba zai soki Rasha ba game da ikirarin da aka yi na ta tsoma hannu a zaben Shugaban Kasar Amurka da aka yi a shekarar 2016.

Trump ya ce, ya mika wa Putin sako baki da baki. Putin ya bayar da hankali kan wannan magana kuma ya nuna karsashi  kan batun matuka.

Ya kuma bayyana ci gaba da binciken da ake yi a Amurka kan Rasha ta tsoma hannu a zaben Shugaban Kasar da cewa, babbar musiba ce ga kasarsu wanda abu ne da ya nesanta kasashen 2 da juna.

Da ya ke tabo batun Siriya Trump ya ce, rikicin kasar na da rikitarwa kuma "Hadin kan kasashensu 2 ya kubuytar da rayukan dubunannan daruruwan Siriyawa. kuma ba za su ba wa Iran damar amfana da yakin da suke yi da Daesh ba. Sun kusa kammala kakkabe Daesh daga yankin."

Shugaba Trump ya kuma tabo batun takunkumin da suka kakaba wa Iran da cewa yana da muhimmanci.

Sannan game da Isra'ila kuma ya ce, Shugaba Putin ma yana taimakawa Isra'ila. Dukkansu sun tattauna da Benjamin Netanyahu kuma su ma suna son su yi wani abu game da tabbatar da tsaro a Siriya.

A jawabin da Shugaban Kasar Rasha Vladmir Putin ya yi a wajen ya ce, an yi ganawar cikin aminta da juna kuma ta yi amfani tare da nasara.

Putin ya ce, sun tattauna kan batutuwan da suka shafi alakar rasha da Amurka da kuma makomarsu a nan gaba wanda suka wuce wani lokaci mai matsatsi, kuma babu wata manufa mai kyua da ta sanya aka yi wannan rikici. A lokaci mai tsawo yakin cacar baki ya kare. Rikicin tunani da kasashen 2 suka yi ya dade da wuce wa. Yanayin duniya ya sauya baki daya.

Shugaban na Rasha ya ce, a yau Kasarsa da Amurka na fuskantar matsaloli da dama kuma idan aka hade kokarin bangarorin 2 wje guda to za a shawo kan matsalolin. 

Ya ce, wannan tattaunawa da suka yi da Trmp ta nuna irin bukatar da suke da ita na a kawo karshen rikicin da suke fuskanta.  An kuma dauki matakin da zai kawo karshen rikicin.

Putin ya kuma ce, yadda Rasha da Amurka suka mallaki makaman Nukiliya na nuni da akwai babban alhak,n tabbatar da tsaro a duniya da ke wuyayensu kuma tattauna kan hana yaduwar makaman kare dangi na da muhimmanci kuma sun ika wa Amurka wasu takardu kan wannan bukata.

Putin ya kara da cewa, za su ci gaba da hada kai don yaki da ta'addanci da kuma yaki da kutse a yanar gizo.

Trump ya karkare jawab,in nasa da cewa, ya sha fada kuma yana sake maimaitawa Rasha ba tsoma baki ko hannu a zaben Shugaban Kasar Amurka na 2016 da ya kawo trump kan mulki ba. Rasha ba ta taba yin wani abu da zai hargitsa Amurka ba.

 Labarai masu alaka