Koriya ta Kudu da ta Arewa sun dauki sabon matakin wanzar da zaman lafiya

Koriya ta Arewa ta sake cika alkawarin da ta yi wa makociyarta ta Koriya ta Kudu da Amurka bayan sun gudanar da manyan taruka a wannan shekarar.

Kasashen Koriya sun dawo da alakar sojinsu a iyakar yammacinsu, kamar yadda Ma’aikatar Tsaro da ke Seoul ta sanar.

Ma’aikatar ta tunatar da yarjejeniyar da aka kulla da shuganata Moon Ja-en a ranar 27 ga watan Afrilun a loakcin da ya gana da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un.

Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya ce, a daidai lokacinda aka dawo da sadarwa a iyakar yamma, wannan ani bangare ne na yarjejeniyar da aka kulla a Panmunjom, wannan zai bayar da goyon baya wajen warware takaddamar da ke tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa.

A nan gaba kasashen 2 za su kafa cibiyar sadarwa a tsakaninsu a bangaren iyakokin gabas sannan za su kwashe tankokin yaki daga kan iyakokin.

Koriya ta Arewa ta kuma amince da ta bayar da gawarwarkin sojin Amurka wadanda suka yi yaki a tsakanin 1950-1953.

Kim ya amince da hakan bayan ya gana da Trump a ranar 12 ga watan Yuni.Labarai masu alaka