Turkiyya ta la'anci tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a Najeriya

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da sanarwa inda ta la'anci tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a Najeriya tare da kashe akalla mutane 20.

Ma'aikatar ta ce, Turkiyya na bakin cikin samun labarin kai hare-haren a lokacin bikin Sallah inda aka kashe tare da jikkata mutane da dama a yankin Damboa na jihar Bornon arewa maso-gabashin Najeriya.

Sanarwar ta yi Addu'ar jin kai ga wadanda suka mutu da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka sami raunuka.

Rahotanni sun ce, an kashe akalla mutane 20 tare a jikkata wasu 48 a harin da aka kai a yankin Damboa na jihar Borno da ke a arewa maso-gabashin Najeriya.

Wasu mata 2 'yan kunar bakin wake ne suka kai harin a lokacin da ake gudanar da bukukuwan Sallah Karama.Labarai masu alaka