Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudirin neman kare hakkokin Falasdinawa

Babban Zauren Majalisar Dinkin DUniya ya amince da kudirin da aka gabatar masa na neman kare hakkokin al'umar kasar Falasdinu.

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudirin neman kare hakkokin Falasdinawa

Babban Zauren Majalisar Dinkin DUniya ya amince da kudirin da aka gabatar masa na neman kare hakkokin al'umar kasar Falasdinu.

Sakamakon yunkurin Turkiyya tare da taimakon Aljeriya ya sanya Majalisar yin zama na musamman don tattauna batun Kasar Falasdin da halin da Falasdinawa suke ciki.

A zaman da aka yi a Zauren Majalisar an gabatar da kudirin kare hakkokin falasdinawa ta hanar jefa kuri'a inda aka amince da shi.

Amurka dai ta yi amfani da karfin ikonta a Kwamitin Tsaro na Majalisar wajen hana amfani da kudirin a baya amma a yanzu an amince da shi a Babban Zaure.

Kasashe 120 ne suka amince da kudirin.Kasashe 8 ne kawai suka nuna rashin amincewa. Kasashe 45 kuma ba su jefa kuri'a ba. Kasashen da suka nuna kin amince wa su ne: Amurka, Isra'ila, Ostireliya, Marshall Ailan, Nauru, Togo, Solomon Ailan da Tarayyar Mikronoziya.

Haka zalika an yi watsi da neman soke sukar da Amurka ta yi wa kungiyar Hamas.

A bayanin da ya yi bayan amicewa da kudirin, Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya ya ce kasashen duniya sun nuna adalci tsagwaronsa. Wannan nasara ce babba. 

Hukunin ya tanadi a cikin kwanaki 60 Majalisar Dinkin Duniya ta kare rayuwaka da dukiyoyin Falasdinawa sanna Isra'ila ta dkatar da kashe wa da zaluntar Falasdinawa ta kuma bude hanyoyin Zirin gaza da ta yi wa kawanya.

 Labarai masu alaka