Erdoğan: Bakin ciki ne zai kashe Amurka game da nasarar Falasdin a Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa, amince wa da kudirin dokar kare Falasdin a Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Amurka shiga halin kunchi da damuwa matuka.

Kakakin Shugaban Kasar Ibrahim Kalin ya bayyana matakin a matsayin nasara gagaruma.

Kalin ya ce Turkiyya za ta ci gaba da tare da Kasar Falasdin wajen kare hakkokinta.

A gefe guda kuma Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da sanarwa kan batun inda ta ce "Kasashen duniya masu hankali mai kyau sun sake nuna wa duniya ba za a kyale Kasar Falasdin ita kadai ba."

Sanarwar ta kara da cewa ana sauraren Sakatare Janar na Majalisar Dİnkin Duniya da ya aiwatar da matakin da aka dauka.Labarai masu alaka