Trump ya gana da Kim a Singapore

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya gana da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un.

Trump ya gana da Kim a Singapore
Bidiyon ganawar Trump da Kim
Bidiyon ganawar Trump da Kim

Bidiyon ganawar Trump da Kim

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya gana da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un.

Trump da Kim sun gana a otel din Capello da ke tsaunin Sentosa a Kasar Singapore.

An fara taron ta hanyar gaisawar shugabannin 2 da misalin karfe 9 na safiya a gogon Singapore. 

Kafin ganawar Shugabannin 2 sun yi dan takaitaccen jawabi ga 'yan jaridu.

Shugaban Amurka Trump ya ce, tattaunawar za ta yi nasara. Yana jin mutuntawa. Akwai kyakkwar alaka za ta kullu ba kokwanto.

Shi ma Shugaban koriya ta Arewa Kim ya ce, ya ji dadin kasancewar sa a wajen. Tunani da Zatonsu na baya ya hana su ci gaba. A yau sun tsallake wannan abu ga su a wajen taron.

Bayan haka ne sai Shugabannin 2 suka wuce dakin da za su gana da juna.

Tattaunawar ta dauki kusan mintuna 45.

A yayin ganawar  babu kowa a tare da Shugabannin sai masu yi musu fassara.

Bayan ganawar shun tsokaci game da abun ya wakana a tsakaninsu.

Trump ya ce, tattaunawar ta yi kyau sosai kuma alakarsu ta inganta matuka.

Shugaban Koriya ta Arewa kuma cewa, ya yi sun ziyarci wajen da kyakkyawar niyya.

Ana sa ran bangarorirn 2 za su gana wa ta musamman da 'yan tawagarsu.

Babban batun ganawar Shugabannin shi e batun sarrafa wa da gwada harba makaman Nukiliya da Koriya ta Arewa ke yi.Labarai masu alaka