Kazakistan ta yi kira da a kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa

Wakilin Kazakistan a Majalisar Dinkin Duniya Kayrat Umarov ya yi kira ga Kasashen Duniya da su dauki matakan gaggawa wajen kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa da ake yi a Zirin Gaza.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Kazakistan ta fitar ta bayyana cewa, a jawabin da Umarov ya yi a zaman da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kan rikicin Falasdin da Isra'ila ya ce, suna bakin ciki game da kisan gillar da aka yi a yayin zanga-zangar lumanar da Falasdinawa suka gudanar a Zirin Gaza.

Ya ce, Kazakistan na kira ga kasashen duniya da su kawo karshen wannan rikici wanda ke janyo zubar da jini da rasa rayuka.

Umarov ya yi kira da a ayi amfani da hankali wajen guje wa duk wani abu da zai sake rura wutar rikici tsakanin bangarorin kuma akwai bukatar a bar Birnin Kudus a Matsayinsa na Birnin Mai tarihi. 

Jakadan ya ci gaba da cewa, Kazakistan na tare da duk wani hukunci da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yanke kuma suna goyon bayan amfani da hanyoyi na siyasa wajen warware rikicin.

A zanga-zangar da aka yi a Zirin gaza mutane 63 ne suka yi Shahada yayinda wasu dubu 2,770 suka samu raunuka. Daga cikin wadanda suka yi Shahadar akwai yara ‘yan kasa da shekaru 18 su 8, kuma daga cikin wadanda suka jikkata akwai yara 225 da mata 86. Labarai masu alaka