Birtaniya ta ce ba ta amince a mayar da ofishin jakadancin Amurka a Isra'ila Kudus ba

Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa, Kasarsa ba ta amince da matakin da Amurka ta dauka na mayar da ofishin jakadancinta da ke Isra'ila zuwa Kudus ba.

Boris Johnson ya tattauna ta wayar tarho da Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas.

Kamfanin dillancin labarai na Falasdin WAFA ya bayar da labarin cewa, a tattaunawa Johnson ya shaida wa Abbas cewa, Birtaniya ta amince da matakin da Amurka ta dauka ba, kuma suna mika ta'aziyyar mutanen da aka kashe a Zirin gaza tare da kasancewa a shirye don taimaka wa a samu zaman lafiya.

Shugaban Falasdinawa  Abbas kuma ya ce, ya ji dadi tare da gamsuwa da matakin da Birtaniya ta dauka kuma Falasdin ta tare da duk wani yunkurin kasa da kasa da zai samar da zaman lafiya ta hanyar adalci.

Falasdinawa 63 ne suka yi Shahada bayan bude musu wuta da sojojin Isra'ila suka yi a Zirin Gaza a lokacin da suka taru don nuna adawa da dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa Kudus da kuma cika shekaru 70 da Nakba.Labarai masu alaka