Amurka ta gana da Turkiyya akan harin Siriya

Wakilin ma'aikatan harkokin wajen Amurka John Sullivan ya kira mai bada shawara akan harkokin wajen Turkiyya Ümit Yalçın inda suka tattauna karon farko akan harin da haɗakar kasashen Amurka, lngila da Faransa suka kaiwa gwamnatin Asad.

Kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert ta sanar a rubuce baya ga tattaunawar Sullivan da Yalçın an kuma maganta da ministocin harkokin wajen ƙasashen Kuwait Sabah Al Hamad al Sabah, Czech Martin Stropnicky da kuma na lraqi lbrahim al Jaferi.

Kafin kai harin shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya gana da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ta wayar tarho akan lamarin.

Jiragen yaƙin Amurka, lngila da Faransa sun kai hari ta ruwa da sama ga gwamnatin Asad a gurare uku da makamai masu linzami 105.Labarai masu alaka