"Trump na neman ya sulhunta da Rasha"

An bayyana cewar akwai alamun Rasha da Amurka zasu sasanta tsakaninsu.

"Trump na neman ya sulhunta da Rasha"

An bayyana cewar akwai alamun Rasha da Amurka zasu sasanta tsakaninsu.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewar shugaban Amurka Donald Trump nada bukatar sasantawa da Rasha.

Kamar yadda Putin ya shaidawa manema labarai ya kamata kasashen biyu su sulhunta tsakaninsu tare da gyara dangantakar dake tsakaninsu.

Putin ya bayyana cewar basa ganin Amurka amatsayar makiya amma 'yan majalisar Amurkan sun sanya Rasha a cikşn jeren kasashen makiyarsu.

Shugaban na Rasha ya tabbatar da cewa Rasha bata taba yin katsalandar a harkokişn wata kasa ba amma kowa ya san da cewa a duk lokacin zabe a Rasha amurka na ruwa da tsaki

Putin ya kara da cewa shugaba Donald Trump ya buktar gyara hurdar kasashen biyu amma akwai masu hana ruwa gudu.

 Labarai masu alaka