'Yan darikar Gonabadi sun yi artabu da jami'an tsaron Iran

Sakamakon kama shugaban Tarikar Gonabadi da ke Iran Niimatullah Reyahi ya sanya magoya bayan Tarikar artabu da jami'an tsaro a Tehran Babban Birnin Kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Iran IRNA ya bayar da labarin cewa, kakakin 'yan sandan kasar Sait Muntezirulmehdi ya ce, daya daga cikin masu zanga-zangar ya kutsa kai kan 'yan sanda da motar bas tare da kashe jami'ai 3.

Muntezirulmehdi ya kara da cewa, an kama mutumin da ya kashe 'yan sandan tare da wasu karin mutane 8 da ke adawa da gwamnati.

Ya kara da cewa, an shawo kan lamarin a yankin kuma jami'an tsaro sun dauki dukkan matakan hana sake afkuwar abu makamancin wannan.Labarai masu alaka