Wani kare dan jam'iyyar SPD ta Jamus zai jefa kuri'ar zabe

A wata wasika da aka aike wa wani kare dan jam'iyyar SPD ta Jamus an bayyana masa cewa, zai iya jefa kuri'a a wajen zaben yarjejeniyar shiga gwamnatin hadaka.

Jam'iyyar SPD ta amince ta kafa gwamnatiin hadaka tare da jam'iyyar CDU inda nan da yammacin 6 ga watan Fabraru ne 'yan jam'iyyar suka sami damar jefa kuri'a game da shiga kawancen.

Sakamakon haka ne jaridar Bild ta Jamus ta rawaito jam'iyyar SPD na yunkurin ba wwa karen damar jefa kuri'a wanda da ma dan jam'iyyar ne.

Jaridar ta ce, a ranar 6 ga watan Fabrairu ne aka yi wa karen rejista a jam'iyyar.

Hausawa dai na cewa, idan da ranka za ka sha kallo.

Tag: Karya , Kare , 'Yanci , Jamus

Labarai masu alaka