Shugaba Erdoğan ya aike da sakon ta'aziyya ga Iran

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya aike da sakon ta'aziyya ga takwaransa na Iran Hassan Ruhani sakamakon mutuwar mutane 66 a hatsarin jirgin kasa da ya afku a kasar.

A wasikar ta Erdogan ya bayyana cewa, ya yi bakin ciki a lokacin da ya samu labarin hatsarin jirgin, kuma yana Addu'ar samun jin kai ga mutanen 66 da suka rasa rayukansu.

Erdogan ya kara da cewa, Turkiyya na jin irin radadin da al'umar Iran suke ji, kuma Turkiyya a shirye ta ke da ta bayar da duk wani taimako da Iran ke bukata.Labarai masu alaka