MDD: An kubutar da yara dubu 5 da aka tursasa wa yin yaki a kasashe 20

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, a kasashe 20 da ake yin yaki an saki yara kanana dubu 5 a a shekarar da ta gabata amma kuma duk da ahaka akwai dubunnan wasu da ke ci gaba da yaki.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Yara Kanana da Hare-Hare Virginia Gamba ta fitar da rubutacciyar sanarwa a wani bangare na bukukuwan ranar yaki da saka yara kanana a harkokin yaki da duniya inda ta ce,, a yankunan da ake rikici akwai dubunnan yara kanana maza da mata a hannun kungiyoyin da ke rikici da juna wanda suke amfani da su a matsayin mayaka.

Ta kara da cewa, sakamakon yunkurin da suke yi, a shekarar da ta gabata a kasashen duniya 20 da ake yaki an kubutar da yara kanana maza da mata da dubu 5 daga hannun wadanda suka tirsasa musu yin yaki, kuma yaran sun samu matsala sosai tare da shiga halin kaka nika yi.

Gamba ta kuma ce, a kasashen da aka fi saka yara kanana yaki akwai Afganistan, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Iraki, Myammar, Najeriya, SOmaliya, Sudan ta Kudu, Siriya da Yaman.Labarai masu alaka