Putin: Shugaban Koriya ta Arewa ya samu nasara kan Trump

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya yi nasara kan Donald Trump a rikicşn da suke yi kan tsibirin Koriya.

Putin: Shugaban Koriya ta Arewa ya samu nasara kan Trump

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya yi nasara kan Donald Trump a rikicin da suke yi kan tsibirin Koriya.

Kafafan yada labarai na Rasha sun rawaito Putin a lokacin da ya ke amsa tambayoyinsu inda ya ce 

"Hakika Shugaba Kim jong-Un ya samu nasara a wanna zagayen. Ya warware matsalolinsa. Yana da makaman Nukiliya da ka iya tafiyar kilomita dubu 13 wanda hakan ke nufin da zai iya maganin duk wasu abokan d-gaba da ke doron kasa a ko'İna suke."

Putin ya ce, yana son tausasa zuciyar Kim inda ya bayyana shida dan siyasa mai hankjali kuma masanin ya kamata.



Labarai masu alaka