Netanyahu ya shiga tsaka mai wuya

A karo na 6 Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sake shiga komar 'yan sandan kasar sakamakon zargin cin hanci da ake masa inda a ya sake bayar da shaida a wannan karon.

Netanyahu ya shiga tsaka mai wuya

A karo na 6 Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sake shiga komar 'yan sandan kasar sakamakon zargin cin hanci da ake masa inda a ya sake bayar da shaida a wannan karon.

Sanarwar da rundunar 'yan sandan Isra'ila ta fitar ta ce, sun tuhumi Netanyahu na tsawon wasu awanni a ofishinsa da ke birnin Kudus.

Sanarwar 'yan sandan ba ta bayar da wani dogon bayani ba  amma kafafan yada labaran sun ce, an dauki tsawon awanni 4 ana yi wa Netanyahu tambayoyi.

Bayan tambayoyin Netanyahu ya fitar da wata sanarwa ta shafinsa na Twitter inda ya ce, kalaman da ya ke yi tun lokacin da aka fara bincikarsa game da cin hanci da rashawa su zai maimaita, wato "Babu wani da za a samu saboda ba komai aka yi ba."

A makon da ya gabata ma 'yan sandan Isra'ila sun yi wa Netanyahu tambayoyi.

A baya ma matar Netanyahu Sarah Netanyahu ta bayar da shaida a gaban 'yan sanda game da zargin cin hancin da ake wa mijinta.

 Labarai masu alaka