Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Saudiyya da Iran su rage adawar da ke tsakaninsu

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen Saudiyya da Iran da su sassauta rikicin da ke tsakaninsu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Saudiyya da Iran su rage adawar da ke tsakaninsu

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen Saudiyya da Iran da su sassauta rikicin da ke tsakaninsu.

Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Stephane Dujarric ya bayyana wa manema labarai cewa, suna kira ga kasashen da su mayar da wukakensu tare da rage zafin adawar da ke tsakaninsu.

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka harba makami mai linzami zuwa arewacin Riyadh daga kasar Yaman, kuma Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman ya dora alhakin wannan abu kan 'yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran.

Iran kuma ta musanta wannan zargi na cewa, tana ba wa mayakan Houthi makamai masu linzami.Labarai masu alaka