• Bidiyo

China da Amurka zasu magance matsalar Koriya ta Arewa

Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewar sun aminta tare da Amurka akan yadda zasu warware matsalar Koriya ta Arewa.

China da Amurka zasu magance matsalar Koriya ta Arewa

Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewar sun aminta tare da Amurka akan yadda zasu warware matsalar Koriya ta Arewa.

Xi tare da shugaba Trump dake ziyarar kwanaki uku a kasar sun gudanar da taron manema labarai inda suka bayyana shirinsu akan warware matsalolin tsaro, nukiliya da kuma diflomasi.

Baya ga bunkasa lamurkan tattalin arziki sun aminta akan aiki bai daya don kawo karshen lamarin Koriya ta Arewa.

A taron shugaban kasar Amurkan Donald Trump ya bayyana kudurin kasarsa wajen kara inganta dangantaka ta kasuwanci da tsaro da kasashen yankin Pasifik.Labarai masu alaka