An cire wa Le Pen rigar kariya saboda yada hotunan 'yan ta'addar Daesh a yanar gizo

Majalisar Dokokin Faransa ta cire rigar kariyar Shugabar Jam'iyyar NFP Marine Le Pen sakamakon samun ta da laifukan yada hotunan 'yan ta'addar Daesh a shafinta na Twitter shekara 2 da suka gabata.

A shekarar 2015 Marine Le Pen ta yada wasu hotuna 3 na 'yan ta'addar Daesh a shafinta na Twitter, sakamakon haka mai gabatar da kara na Nanterre ya fara bincikarta.

Majalisar dokokin ta cire rigar kariyar dan majalisa mai tsaurin ra'ayi Gilbert Collard saboda aikata irin wannan laifi.

Majalisar Tarayyar Turai ma sau 5 tana cire wa Le Pen rigar kariyarta.

Cire rigar kariyar dai zai ba wa hukumomi damar gurfanar da Marine Le Pen a gaban kuliya.Labarai masu alaka