Saudiyya za ta sayi garkuwar kariya daga makamai masu linzami samfurin S-400 daga Rasha

Gwamnatocin Saudiyya da Rasha sun amince tare da sanya hannu kan wasu yarjeniyoyin aiyukan soji na zamani inda za a yi kasuwancin makamai da kayan kariya.

Sanarwar da Kamfanin Samar da Makamai na Saudiyya da Kamfafanin dillanci labaran kasar suka fitar na cewa, kamfanin na Saudiyya ya sanya hannu da takwaransa na Rasha Rosoboronexport kan yarjejeniyar sayen makamai da kuma horar da sojoji.

A labaran an ce, an amince da sayen Manyan motocin harba makamai masu linzami samfurin TOS-1A, Kornet-EM, bindigar AK-103 da garkuwar makamai masu linzami samfurin S-400.

An bayyana cewa, yarjejeniyar da Rosoboronexport ya cimma da Saudiyya za ta ba wa kamfanununnukan samar da makamai na Saudiyya samun dama wajen kara habaka da samun horo.

 Labarai masu alaka