Iran ce musabbabin ziyarar sarkin Saudiyya a Rasha

An bayyana cewa sarkin Saudiyya Salman bin Abdelaziz ya ziyarci Rasha ne domin tattaunawa da shugabanin kasar akan yadda Iran ke tasiri a yankunan, abinda ke cimma Saudiyyar tuwo a kwarya.

Iran dai ta hada karfi da karfe tare da kasar Rasha wajen canja tsarin siyasar gabas ta tsakiyya dama yankunan baki daya. Hankalin Saudiyya bai kwanta da irin wannan dama da Iran ta samu ba.

Haka zalika Iran da haddin gwiwar Rasha tana goyun bayan shugaban Siriya Bashar Asad, lamarin daya sa rikicin kasar taki ci taki cinyewa.

Sarki Salman Abdulaziz shine sarkin farko daya taba ziyartar Rasha daga Saudiyya, hakan na nuni da irin rawar da Rasha ke takawa a gabas ta tsakiyya a zamanin mu a yau.

TRT World

 Labarai masu alaka