An nemi Barzani daya soke zaben raba gardamar Arewacin Iraqi

Daya daga cikn mataimakan firaministan Turkiyya Bekir Bozdağ yayi kira ga shugaban Kurdawan Arewacin Iraqi Masoud Barzani daya gaggauta soke zaben raba gardaman da aka gudanar a yankin ba bisa ka'ida ba.

An dai gudanar da zaben raba garda a Arewacin Iraqin don samar da 'yancin kai ga yankin a watan jiya, sai dai dayawan kasashe basu goyi bayan yin hakan ba, inda suke ganin hakan ka iya gurbata lamarin yaki da ta'addanci da akeyi a yankunan.

Bozdağ ya kara da cewa ya kamata Masoud Barzani ya bi hanyar lumana wajen warware dukkanin matsalolin dake tsakaninsu da kasar Iraqi.

AALabarai masu alaka