Yadda ake miyan jan Lentil a Turkiyya

Wannan miyan ana kiransa da sunan “kırmızı mercimek çorbası” watau miyan jan lentil. Wannan miyan da ake yi a kusan ko wani gida da kuma ko wani gidan abinci ba mamaki ya kasance miyan da aka fi sha a kasar.

Yadda ake miyan jan Lentil a Turkiyya

Barkanmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirinmu mai taken abincin Turkiyya. Daga cikin nau’o’in abincin kasar Turkiyya miya ya kasance mai tasiri kwaran gaske. Miya dai ya kasance yariman abinci ada dama yanzu tun daga gidajen gwamnati, gidajen masu hannu da shuni har izuwa gidajen talakawa a kasar Turkiyya. A yayinda a wasu al’adun miya ana amfani da shi ne a lokacin cin abincin rana ko dare, a Turkiyya kuwa ana anfami da miya ne a duk lokacin cin abinci, har a lokacin kalaci ko karin kummalo. Wannan lamari ne da ya zama tamkar al’ada a kasar Turkiyya. Idan aka kwatanta miyan kasar Turkiyya da na sauran kasashe za’a ga cewa miyan kasar Turkiyya ya kunshi nau’o’i daban-daban yana kuma kunsar kayayyaki da dama a lokacin yinsa. Alal misali, idan muka dubi ire-iren miyan kasashen yamma zamu ga cewa ana yawan yinsa ne da ruwa-ruwa, miyan kasar Turkiyya kuwa ana yinsa ta fannoni daban-daban ko dai da ruwa-ruwa ko da kauri, ana yinsa kuma da sanyi ko da zafi. Amma daga cikin wadannan nau’o’in miyan kasar Turkiyya akwai wanda ya zama akan gaba ala külli halin. Wannan miyan ana kiransa da sunan “kırmızı mercimek çorbası” watau miyan jan lentil. Wannan miyan da ake yi a kusan ko wani gida da kuma ko wani gidan abinci ba mamaki ya kasance miyan da aka fi sha a kasar. A yau zamu bayyana muku yadda ake sarrafa wannan miya mai dadi da saukin yin.

 

Domin yin “Kırmızı mercimek çorbası”  watau miyan jan lentil ana bukatar wadannan kayayyaki,

  • Kofi 1, 5 na jan lentil
  • Cokali daya na man shanu
  • Cokali daya na nikekken tumatir
  • Albasa daya da aka yayyanke
  • Karamin cokali daya na nikekken jan borkono
  • Rabin karamin cokali na nikekken bakin borkono
  • Cokali daya na gishiri
  • Karamin kofi shidda na ruwa garwaye da maggi

 

Yanzu kuma sai yadda ake sarrafawa;

Da farko dai za’a wanke lentil din a cikin ruwa sai ya wanku sosai. Bayan haka sai a fara soya albasa a cikin mai. Daga bisani kuma sai a zuba nikekken tumatin din a ci gaba da soyawa. Bayan ‘yan mintuna sai a zuba lentin din a ciki a ci gaba da soyawa. Bayan mintuna biyu kuma sai a zuba ruwan maggin mai zafi a cikin lentil din da ake soyawan. Bayan an kara sauran kayan yaji da sunka hada da borkono da gishiri sai a tsagaita wutan murhu a ci gaba da dafawa na tsawon rabin awa har sai lentil din yayi laushi. Bayan ya dafu ya yi laushi sai a tace a kuma raba.

A sha lafiya.

 Labarai masu alaka