Tarihin hukumar bayar da tallafin karatu (YTB) ta kasar Turkiyya

Daga wannan makon zamu fara bayyana muku ire-iren muhimman ayyukan cigaba da hukumar bayar da tallafin karatu ga Taliban ƙasashen waje a Turkiyya watau YTB ke gudanarwa a fadin duniya.

Tarihin hukumar bayar da tallafin karatu (YTB) ta kasar Turkiyya

 A cikin wannan shirin namu na hukumomin ci gaban Turkiyya daya ƙunshi ayyukan hukumar bayar da tallafin karatu ga ɗaliban ƙasashen waje a Turkiyya, Ƙungiyar bayar da agajin gaggawa ta Turkiyya, Hukumar Yunus Emre da  kuma hukumar haddin kai da taimako na Turkiyya watau TlKA, a makonni huɗu da suka gabata mun bayyana muku ire-iren ayyukan da hukumar TlKA ke gudanarwa a fadin duniya.

Daga wannan makon zamu fara bayyana muku ire-iren muhimman ayyukan cigaba da hukumar bayar da tallafin karatu ga Taliban ƙasashen waje a Turkiyya watau YTB ke gudanarwa a fadin duniya.

Da farko dai, Hukumar YTB an kafa ta ne a ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 2010, wacce aka ɗorawa nauyin kula da taimakawa Turkawa mazauna ƙasashen waje, ƴan uwa Turkawa ƴan wasu ƙasashen da kuma bayar da tallafin karatu ga ɗaliban ƙasashen waje dake karatu a ƙasar Turkiyya.  

Hukumar bayar da tallafin karatu da kuma kulla da Turkawa mazauna ƙasashen waje da kuma yan uwa Turkawa ƴan wasu ƙasashen watau YTB nada nauyin kula da Turkawa mazauna ƙasashen waje, Turkawa ƴan wasu ƙasashe ta hanyar samar da hanyoyin da zata bunƙasa harkokin kasuwancin su, al'adun su da kuma sauran ayyukan su na yau da kullum. Bayan haka hukumar na kuma dauke da nauyin bayar da tallafin karatu ga ɗaliban ƙasashen waje dake karatu a fadin ƙasar Turkiyya.

A bisa wadannan muhimman ayyukan hukumar ne zamu bayyana muku ire-iren muhimman rawar dake takawa domin ci gaban bil'adama a fadin duniya a cikin ƴan makonnin nan.

Ku huta lafiya.

 

 Labarai masu alaka