Al'umar Moro na kan hanyar fita daga kangin wahala

Sharhin Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa  dake Jami'ar Yildirim Beyazit Ferfesa Kudret BÜLBÜL.

Al'umar Moro na kan hanyar fita daga kangin wahala

Sharhin Al'amuran Yau da Kullum: 6

Yankin Moro ba mamaki na ɗaya daga cikin yankunan da aka fi tattauna wa akai, a tarihin ɗan Adam. A farko farko shekarar 1500 an rasa mutane da dama, a yayinda yankin ya ci gaba da kasancewa cikin matsalolin zubar da jini, zalunci da kashe-kashe. Yaran yankin Moro sun fara ganin hasken kauda matsalolin ukuba, zalunci da maraitan da suka kasance a ciki.

                                      

A cikin wannan sabuwar maudu'in mun sake kasancewa tare da shugaban tsangayar siyasa  dake jami'ar Yıldırım Beyazıt Ferfesa Kudret BÜLBÜL.

 

Moro, ɗaya daga cikin yankunan da ake magana da harshen Turkanci, ya kasance yana fuskantar zalunta tamkar ƙasashen Falasɗinu, Eritrea da Kashmir. Ba mamaki babu lamarin da ya bayyana irin kisan kiyashin da ake yi a Moro kamar yadda sha'iri Salih Mirzabeyoğlu ya zayyana a wani sha'irinsa mai taken “Jaruman Moro akan yaƙin kwatan ƴanci” amma Musamman yankin Moro na bukatar fiye da ire-iren waɗannan matakan da sha'irin ya bayyana.

Anan muna magana ne akan zaɓen raba gardaman da aka gudanar a ranar 21 ga watan Janairu.

 

Takaitaccen Tarihin Moro

Wannan tsibirin Musulmi a ƙasar Filipin bai kasance da wani bambanci ba idan aka kwatanta shi da sauran ƙasashen gabashin duniya. Al'umman ƙasar Moro dai Musulmai ne masu amfani da al'adun lslama. A wannan yankin, Musulmi na zaune a kasarsu har izuwa shekarar 1500. Musulman Moro sun soma yaƙi da ƙasar Spain ne a shekarar 1521. Bayan rushewar Andalusia yaƙin ya yaɗu har zuwa ƙasar Filipin daga wannan ranar kawo yanzu ne kusan shekaru 500 kenan da ake ci gaba da samun sauye-sauyen da muke gani a yankin a halin yanzu. A yayinda a shekarar 1900 Musulman yankin Kudancin Filipin suke masu rinjaye , sabilil da matakan kakagidan da ƙasar ta dauka a wannan lokacin ya sanya Musulmai kasancewar marasa rinjaye a fadin ƙasar.

Kasancewar yankin a hannun Spain a baya, wanda kuma ya kasance ƙarƙashin kulawar Amurka a ƙarni na 20 da kuma mamayewar Filipin daga baya sun haifar da hallakar Musulmi ko kuma tilasta su yin hijira daga yankin

A lokacin da nakai ziyara a Cotaboto a shekarar 2016 naga yadda mutanen da aka fitar daga matsuguninsu suke haƙa kwalekwale a saman rafi inda suke zaune domin an hanasu filayen zama.

A shekarar 1960 ne Musulman Moro sunka fara kafa ƙungiyoyin da zasu kare su daga dukkan matakan da ake ɗauka domin kauda su daga doron kasa. Ɗaya daga cikin wadannan kungiyoyi shi ne Ƙungiyar Kwatar Ýancin lslama da Selamet Hashim ke jagoranta wanda bayan rasuwar sa a shekarar 2003 magajin shi Haj Murat lbrahim ya ci gaba da jan ragamar Ƙungiyar.

A shekarar 2012 ne gwamnatin Filipin da kungiyar suka rataɓa hannu akan yarjejeniyar kawo karshen yaƙin basasar shekaru 40 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 120 da kuma sanya hijirar fiye da mutane miliyan biyu

A shekarar 2014 kuma anka kirkiro Ƙungiyar kula da ƴancin kai. A yayin yaƙin neman zaɓen da aka gudanar a shekarar 2014 shugaban ƙasar Filipin Duterte ya yi alƙawarin baiyi yankin cikekken ƴanci.

 

Sakamakon zaben raba gardama da ma'anarsa

 

A zaben raba gardaman da aka gudanar a ranar 21 ga watan Janairu shekarar 2019 kaso 80 cikin ɗari ne sunka aminta da a baiwa Moro cikekken ƴanci. A sanadiyar haka anka aminta akan bayyana hukumar kafa gwamnatin Bangsamoro da wakilai 80, inda kuma anka aminta da cewa za'a kammala shirye-shiryen kafa gwamnatin ne a shekarar 2022.

ldan aka aminta akan zaɓen raba gardama da aka gudanar kaso 75 cikin ɗari na harajin yankin zai je ne ga ƙananan hukumomi, gwamnatin tarayya kuma ta karɓi kaso 25 cikin ɗari. Haka kuma ma'adanan yankin kaso 75 na ƙananan hukumomi ne kaso 25 kuma na gwamnatin tarayya zasu kasance.

Musulman Bangsamoro zasu kasance daban da al'umar ƙasar Filipin domin zasu tafiyar da gwamnatin su ne akan tsarin lslama. Haka kuma Kiristoci dake yankin zasu bi tsarin gwamnatin Filipin. Yankin Moro a cikin gida zata kasance mai cin gashin kanta, amma a harkokin tsaro da hurɗar ƙasa da ƙasa zata kasance ƙarƙashin gwamnatin Filipin.

 

Buƙatar Musulman Moro

Taimakawa samar da zaman lafiya: A faɗin duniya duk inda ka duba zaka ga cewa samar da zaman lafiya ko yin sulhu abu ne mai wuyan gaske. Wadanda anka yiwa sulhun zaman lafiya zaka ga kuma a koda yaushe suna cikin hatsarin ƙara faɗawa cikin wata sabuwar rikici. A sabili da haka akwai bukatar kungiyoyin ƙasa da ƙasa da su sa baki domin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin ta Filipin. Matakan da shugaban ƙasar Filipin Rodrigo Duterte ya ɗauka na mayar da yankin Moro ƙawa ta gaske kuma mafi kusa da kuma kasancewar zama da yayi a yankin a lokutan samartakarsa da kulla kyakkyawar dangantaka da mutanen yankin nada muhimmanci sosai a yunkurin samar da lumana a yankin.

A sabili da haka taimakon da shugaba Duterte ya bayar da kuma kira da a ayyanar da hakan nada muhimmanci sosai. Ya dai kamata a lura, domin kada Ƙungiyar DEASH ta gurɓata tafiyar.

 

Buƙatar taimakawa marayu da sauran al'umma: Wannan al'umman da ta kwashe shekaru 500 tana fama da ƙalubale tabbas ta kasance mai buƙatun taimako ƙwaran gaske. A yayinda na kai ziyarar dana bayyana a baya naga ƙungiyoyi masu zaman kansu har 26, amma in banda Ƙungiyar bayar da tallafi ta Turkiyya watau IHH babu wata kungiyar kasa da kasa da ke kai taimako a yankin. Hakika, al'umman Moro na cikin buƙatar taimakawa da gudunmawa kwaran gaske. Bari in ɗan yi sharhi akan wani ƙasida da na rubuta a baya wanda za'a iya samun sa ta wannan shafin: (https://www.yenisafak.com/hayat/filipinlermoro-muslumanlari-ve-otesi-2556104)

Musulman Moro a yayinda suke gwagwarmayar samun ƴanci na buƙatar taimako da gudunmowa mai yawa. Wadannan mutanen yankin da suka kwashe ƙarnoni suna fama da yunƙurin samun yanci na bukatar akai musu ɗauki mai gwabi.

Zasu dai kasance cikin buƙatar samar da tsarin mulkin siyasa, kuɗaɗen shiga, gudanarwa, ilimin jami'a, doka da kuma taimakon gina ɗan adam. Kasancewar rashin ingantattun matakai da suka dauka lalurar Musulmi a Moro ta kasance akan masu bayar da gudummawa a cikin yankin kachal. Akwai dai buƙatar su dauki kwararan matakai da zasu sama musu da ilimi, tsarin mulki, Shari'a, gudanarwa, lafiya da makamantansu daga faɗin duniya.

 

Amfanin tallafawa da Turkiyya ke yi domin samar da zaman lafiya a faɗin duniya: Turkiyya ce ta kafa hukumar ƙasa da ƙasa a cikin Moro domin tattaunawa akan hanyar da za'a bi domin samar da zaman lafiya a yankin. Baya ga wannan hukumar ta kuma kafa wata kungiyar da zata kula da yunƙurin samar da lumana a yankin. Daga cikin mutane biyar da suka haɗa wannan kwamiti akwai ƙungiyar ƙasar Turkiyya mai zaman kanta wacce ta kasance a ciki sabili da neman hakan da Musulman Moro sunka yi. Ɗan ƙasar Turkiyya dake ɗaya daga cikin mutanen biyar shi ne Hüseyin Oruç daga Ƙungiyar IHH.

 

Turkiyya, sabili da irin tarihinta, kiman da take dashi a idon duniya ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi ɗaukar matakan samar da zaman lafiya a ƙasashe daban daban a fadin duniya. ire-iren waɗannan matakan samar da lumana da Turkiyya ke yi basu kasance a fuskar ƙasa kawai ba, har ma ta hanyar kungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami'o'i kamar yadda ta yi a Filipin.

A ƙarshe dai, batun da za a iya cimma akan gwagwarmayan samun yanci a shekaru 500 a Moro yana da matukar muhimmanci akan samar da lumana a yankin. Ya kamata mu taimaka wajen cigaba da wannan tsari domin Musulmai a Moro, Filipin da dukkan sauran al'ummar yankin su kawo zaman lafiyar da zaɓen raba gardaman da aka gudanar a yankin ta soma.

 

 

 

   Wannan sharhin ferfesa  Kudret BÜLBÜL ne shugaban kulliyar siyasa a jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt.

                                        Labarai masu alaka