Hattuşaş,daular makiyan Fir'aunonin Masar

Daular Hitit,ta kasance a sahun manyan daulolin da suka mallaki yankin Anatoliya shekaru aru-aru gabanin haifuwar Annabi Issa Allah ya yarda da shi.

Hattuşaş,daular makiyan Fir'aunonin Masar

Daular Hitit,ta kasance a sahun manyan daulolin da suka mallaki yankin Anatoliya shekaru aru-aru gabanin haifuwar Annabi Issa Allah ya yarda da shi.Duk da cewa,karnoni da dama kenan da ta durkushe,amma kawo yanzu babbar helkwatar wannan daular,wato birnin Hattuşaş na ci gaba da haskawa,inda take ci gaba da nuna wa dubban maziyartanta yadda ta kasance katafariya da kuma shahararriya a wani zamanin tarihin mutuanen dauri.

An kafa daular Hitit shekaru 1600 gabanin haihuwar Annabi Issa Allah ya yarda da shi.Kamar yadda aka gano a allunan laka na wancan zamanin, Daular ta kafu kan mulkin demokradiyya a lokuta mabambanta na tarihinta.A wannan daular wacce sarakuna ne ke ja akalar mulkinta,akwai majalisar wakilai mai suna Pankuş wacce ke sa'ido kan mulkin mahukuntan Hitit da kuma samar dokoki tafiyar da kasa.


Daya daga cikin ababen a zo a gani da kabilar Hitit ta yi shi ne samar da yarjejeniya ta farko a tarihin bil adama,wacce ake kira da yarjejeniyar kadeş da ta rattaba wa hannun don samar zaman lafiya tsakanin ta da 'yan daular Masar.Kawo yanzu Hattuşaş cibiyar daular Hitit wacce ta yi matukar ci gaba a fannin siyasa da fasaha, na ci gaba da jan hankalin duniya ga baki 
Hattuşaş,wanda a yau ake kira da Boğazköy  ya kasance a tsakiyar yankin bahar Rum a gundumar Çorum da ke kasar Turkiyya.A yau birnin mai sassa biyu,wato sashen kasa da na sama, ya kasance wani katafaren gidan ajje kayayyakin tarihi.


A sashen kasa na birnin akwai muhallan fararen hula da kuma daya daga cikin manyan wuraren ibadar Hattuşaş,wanda ke kan wani tudu mai tsayin gaske.
A sashe kasa,akwai cocuna masu dumbin yawa, kazalika wannan bangaren ya kasance kewaye da wata babbar katanga mai kofofi hudu.Gumakan Zakunan da ke a bangarori biyu na kofofin da aka kawata da surar wadannan dabbobi, na yin nuni da irin yadda kabilun Hitit suka shahara a fannin aikin hannu.


A tazarar kiloma 2 daga arewa maso gabashin Hattuşaş, haikalin Yazılkaya ya kasance a daya daga cikin wuraren ibada masu kyau da daukar hankali.An kawata katangun Wannan haikalin mai kunshe da dakunan ibada biyu da zanen fuskokin ababen bauta  maza da mata na kabilun Hitit.

Idan har kuka kai ziyara Çorum da nufin leka birnin Hattuşaş,kar ku sake ku koma gida ba tare da kun kashe kwarkwatan idanunku a gidajen ajje kayayyakin tarihi na Çorum da Boğazköy ba,zagayawa a titunan İskilp masu cike makil da ababen tarihi, yada zango a hanyoyin daular Hitit,sheka turaren furrenin de ke wadannan yankunan,dandana dadadan girke-girken gargajiya kamar su dolma da kuma sayen kilisai kalar Kargı-bezi.


Hattuşaş,babban birnin kabilun hitit,daya daga cikin manyan makiyan fir'aunonin masar a fannnonin da suka danganci siyasa da na soja, na nan jiran ku.                                                                                                            Labarai masu alaka