Shin ko dabi'u da tarbiyya sun kawo karshe ne a zamanin yau?

A makon jiya mun yi sharhi akan yadda dabi’u, ka’idoji, mutunci, tarbiyya da kima ke ci gaba da rushewa a cikin al’umma a fadin duniya

Shin ko dabi'u da tarbiyya sun kawo karshe ne a zamanin yau?

SHIN KO DABI’U SUN KAWO KARSHE NE? KASHI NA BIYU

A makon jiya mun yi sharhi akan yadda dabi’u, ka’idoji, mutunci, tarbiyya da kima ke ci gaba da rushewa a cikin al’umma a fadin duniya. Inda muka bayyana cewa babu sunan da ya dace da wannan zamanin da muke ciki da ya fi a kirashi da zamanin karshen dabi’u” watau “the end of values” a harshen Ingilishi. Mun dubi yadda dabi’u suke ci gaba da tabarbarewa da idon basira a fadin duniya, mun bayyana kuma yadda kyakkyawar dabi’u suka kasance marasa tasiri a harkokin Majalisar Dinkin Duniya dama a lamurkan Tarayyar Nahiyar Turai.

A cikin wannan madu’in namu na tabarbarewar dabi’u a fadin duniya zamu ci gaba daga inda muka tsaya a makon jiya.

 

Mun sake kasancewa tare da Malaminmu ferfesa Kudret BÜLBÜL shugaban tsangayar ilimin siyasa a jami’ar Ankara Yıldırım Beyazıt.

 

AMURKA

A ‘yan shekarun da suka gabata, bada wani dadewa ba, zamu iya tuna tafarkin da kasar Amurka ke akai, wanda akafi sani da (american dream) watau “Fatar Amurka” da kuma yadda irin rayuwar Amurka watau (American way of life) sunka kasance abin koyi ga kusan dukkan kasashen duniya. Amma a halin yanzu; da za’a gudanar da binciken jin ra’ayin jama’a game da Amurka, ba mamaki za’a iya ganin kimar kasar Amurka ya yi faduwar da bai taba yin irinsa ba a tarihin kasar.

 

A yau ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka daga kasashen Latin Amurka dubu shidda, wadanda ma aka bayyana kenan, na faman jira wata da watanni a iyakokin kasar Amurka ba tare da an basu izinin shiga kasar ba. A yayinda kasashen Turkiyya, Lebanon, Jordan da kasashen makamantansu ke karban ‘yan gudun hijira fiye da 6000 a dare daya ma, kasar da takasance na daya a duniya ke jinkirtar da dinbin ‘yan gudun hijira da babu wata kasar da take jinkirtar da masu neman mafaka da yawansu yakai hakan ba a duniya. Abin takaici ma kasar dake daya daga cikin kasashe mafi arziki a duniya ke gudanar da haka, har ma yunkurin gina katangar kange ‘yan gudun hijira take yi kamar irin katangar Berlin data rushe a Turai. Abu mafi muni shi ne idan za’a yi lissafi ba mamaki zunzurutun kudaden da za’a bata domin gina katangar; ba zai kai yawan abinda ake bukata domin warware matsalolin ‘yan gudun hijiran da ake neman kangewa ba.

Gwamnatin Amurka na yau ta jefa ka’ida  da dabi’a a cikin kwandon shara, inda ta rungumi akidar “Farko Amurka” da kuma “Sake karfafa Amurka” da kuma tunanin janyewa daga dukkkanin yarjeniyoyin kasa da kasa ba tare da wata cikkakiyar dalili ba. Duniya dai ta zura ido tana kyamar yunkurin janyewar Amurka daga yarjejeniyar Paris ta dumaman yanayi da ma yarjejeniyar ilimi, kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya karkashin UNESCO.

 

A taron kolin Majalisar Dinkin Duniya na bana, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fito karara inda ya bayyana cewar “Muna  kalubalanatar allahiyar duniya” watau yana kyamar kasancewar duniya tsintsiya madaurinki daya. Wannan dai kalamin wani shugaba ne daga cikin kasashe masu tasowa a wasu shekarun da sunka gabata. Fitar irin wannan jumlar daga bakin shugaban kasar Amurka lamari ne da ba’a taba tunanin haka ba. A yau, kasashen yamma har dama Amurka sun kasance kamar suna kare demokradiya, ‘yancin dan adam, hakokin bil adama da dalci, amma a gaskiyar lamari basu kasance ba face masu tafsirin ayoyin Injila baibaye; ta hanyar da su kansu ma ba zai amfanar dasu ba.

 

CHINA -RASHA

Kasashen China da Rasha basu kasance daga cikin kasashen da za’a samu da’a a duniya ba, amma kasar China ta kasance kasar dake bunkasa cikin gaggawa. Kasashen biyu sun kasance masu taka rawa a harkokin siyasar duniya, haka kuma suna da kajera ta din din din a zauren Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya.

Kasancewar yadda lamurkan kasashen biyu ba bude suke ba, ba’a da cikekken sani game da harkokinsu na cikin gida. Ana dai yawan sukar matakan da Putin ke dauka a kan ‘yan adawarsa. Ita kuwa China ba’a cika bayani akan take hakkokin bil adama da mülkin mallakar da take yi a gabashin Turkistan ba sabili da yadda lamurkan kasar sunka kasance a rufe.

 

DUNIYAR ISLAMA

Kasashen Musulmi ma a cikin wannan karnin basu kasance wadanda za’a samu da’a a garesu ba. A yayinda wasunsu ke kan tafarkin ba ruwan mu addini wasu na akan mulkin sarauta wasunsu kuma na karkashin mülkin daular Musulunci. A yayinda kuma wasunsu  ke kan mülkin demokradiyya, wasunsu kuwa na kan mülkin kama karya.

Idan muka dubi kasashen gabas ta tsakiya zamu ga cewa shugabanin yankin basu ma damu da damuwar wadanda suke mulka ba. Sadaukarwar shugabanin kasashen gabas ta tsakiya bata kasance ga al’ummarsu ba, mafi yawan kulawarsu naga masu wuka da nama ne a duniya. Wadannan masu fada a ji a duniya zasu iya tabbatar da hakan ba tare da fargaba ba. Duk da yake basu ne matsalolin wadannan kasashen ba, suna sane da cewa wasu daga cikin kasashen gabas ta tsakiya  na cikin halin ha’ula’in da basu taba samun kansu a ciki ba. A dalilin haka ne wasu daga cikin al’ummar kasashen gabas ta tsakiya sunka zabi ficewa daga kasashensu ko ta halin kaka.

A yau mafi yawan shugabannin kasashen gabas ta tsakiya na kokarin samar da tarbiyar da zata basu damar kalubalantar al’uumarsu, su kuma kare mulkinsu da kujerunsu ko ta wace hali.

 

Ƙarshen nazarin fadakarwa: Daga Frankenstein zuwa fasahar wucin gadi

Labari mai taken “Frankenstein” da wata mata mai suna Mary Shelley ‘yar kasar Ingila ta rubuta a shekarar 1818 a lokacin tana ‘yar shekaru  19, bai kasance labari kawai ba, yana kuma nuna yadda sabuwar nazari ta yi watsi da al’adu, addini da tarbiyya ta kuma sallamawa akidar ‘yan ba ruwamu da addini da nazarin zamani.

A zamanin yau ma, muna cikin irin wannan halin da aka mayar da hankula akan nazarin zamani da kere-keren lamurkan fasahar wucin gadin. Dukkan al’umma dai sunga yadda nazarin zamanin da bai da alaka da dabi’a da tarbiyya ya yi ta’asa a lokacin yakin duniya na farko dana biyu. A halin yanzu ana watsi da dukkan da’a da mutunci da kuma mayar da hankali akan kere lamurkan da sunka fi bil adama karfi ta amfani da fasahar wucin gadi domin kirkirar “mutun-mutumi” Wannan dai bai kasance ba face karshen dan adam da dan adam din ke kirkira da kansa, babu wani sharhi da ya fiye hakan.

Shagaltuwar  Al’umma (Hedonist)

Yadda bunkasa da ci gaban da aka samu a fannonin ilimin kimiya da fasaha, sadarwa, sufuri, akidar rashin addini da wayewa sun sanya kara shagaltuwar mutane a fadin duniya. Mafi yawan matasa basu sanya komai a gaba ba face neman jin dadi da more duniya. Yadda mutane sunka kasance hurdar dake tsakaninsu da abokansu, ‘yan uwansu, iyalinsu, abokan kasuwancinsu, abokan aikinsu, dabbobinsu da yanayin da suke zaune sun ta’alaka ne akan jin dadi da shagali na kara zama abin tsoro a fadin duniya. Lamurkan mutanen yau sun kasance akan sharholiya ba tare da kula da mutunci ko da’a ba, dangantaka da zamunci sun kasance na in akwai kawai tsakanin mutane. Mutumin yau ya kasance hannu mai miya kawai yake lasa.

Gabaki dayan bayanan da muka yi daga makon jiya zuwa yau; sun ta’alaka ne akan yadda kasashe, mutane, ma’aikatu, hukumomi da makamantansu sunka rasa tarbiyya da da’a a tsakaninsu. Sharhin da muka yi bai tsaya ga wasu kasashen da muka ambata ba, bai kuma tsaya ga hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa da muka zayyana ba, bai kuma tsaya ga tabi’un da hallayen da muka furta kawai ba. Wannan matsalar zaizayewar kyakkyawar dabi’u hakika ta zama ruwan dare gama duniya. Tabbas, mutanen da ba’a tsare suke ba amfi samun da’a da tarbiyya tare dasu, akan haka muna fatan afi samun da’a da tarbiyya ga kungiyoyin da ba tsara su ko kirkirosu anka yi ba. Kasancewar yadda muka san cewa duniya na hannun kungiyoyin da aka tsara ne, na sanya mu rasa bege akan samuwar dabi’u a duniyarmu a yau.

A matsayinmu na 'yan Adam, idan ba mu sami sabowar hanyar da za mu dauki matakai; mu kuma dakatar da ƙarshen dabi'unmu a cikin tsari ba, dukkanmu; mu shiryawa mummunar karshen da muka tanadanma kanmu.

 

Wannan sharhin ferfesa Kudret BÜLBÜL ne shugaban tsangayar ilimin siyasa dake jami’ar Ankara Yıldırım Beyazıt, daga nan babban birnin kasar Turkiyya.

                                                             Labarai masu alaka