Majami'ar Nana Maryam (AS)

Majami'ar Nana Maryam (AS), mahaifiyar Annabi Issa Allah ya yarda da shi wanda aka fi sani da "Haikalin Sümela" na a gabashin yankin Bahar Rum na Turkiyya, gaf da wani tsauni mai tsini da tsayin gaske.

Majami'ar Nana Maryam (AS)

A gaf da wani tsauni mai tsinin gaske da ke gabashin yankin Bahar Rum na kasar Turkiyya,akwai wata katafariya kana kyaukyawar majami'a: Haikalin Sümela...

Wannan wurin ibadar ta mabiyan addinin Kiristanci wacce aka gina karnoni 17 da suka gabata,ya kasance daya daga cikin cocuna mafiya tsufa da kuma muhimmanci na duniya.
A cewar labaran da aka rawaito,wasu fastoci biyu wadanda suka fito daga birnin Anthens ne suka gina cocin Sümela a karni na uku na zamanin mulkin kiristanci na Daular Bizans.

 

Sannu a hankali, tsawon shekaru da dama cocin na Sümela ya ci gaba da zama muhimmin wuri.Abinda yasa a karni na 13 miladiya aka sabunta ginin, fadada shi da kuma gina sabbin sassa a cikin sa ta hanyar amfani da makudan kudaden da aka samu.

Bayan gabobin gabashin tekun Bahar Rum sun kasance a karkashin mulkin Turkawa,kamar yadda suka yi a baya,a wannan karon ma sarakunan Daular Musulunci ta Usmaniyya sun kare hakkokin cocin Sümela ta hanyar bai wa malaman cikin sa damar gudanar da aiyukansu salim-alim.
A karni na 18,an sabunta sassa da dama na wannan cocin,inda aka kawata katangun wurin ibadar da zane-zanen masu daukar hankali.A karni na 19, a lokacin da aka kammala gina manyan sorayen wannan cocin,sai majami'ar ta kara kyau sosai.A daidai wannan zamanin ne,martaba da kuma hasken cocin Sümela sun mamaye  duniya.A shekarar 1916 Rashawa sun share shekaru biyu kafin su mamaye gabashin Bahar Rum,inda bayan shekarar 1923 babu wani  mahaluki da yayi saura a wannan muhimmin wurin ibadar.


Ga dai  sassa daban-daban na majami'ar Sümela: Cocin babban tsauni,daidaikun dakunan sujjada,kicin,dakunan dalibai,zauren tarban baki,gidan ajje litattafai da kuma tsarkakkiyar rijiya.An kawata katangun cocin Sümela da illahiran dakunan sujjada da zane-zane masu ban ta'ajibi da daukar hankali.Wadannan zane-zanen wani takaitaccen tarihi ne na manyan lamurran duniya da aka ambata a littafin Injila,rayuwar Annabi Isa da na mahaiyarsa Nana Maryam,Allah ya yarda da su.

 

Cocin Sümela wanda jama'a ke kira da majami'ar Nana Maryam, ya kasance a iyayokin gundumar Maçka na jihar Trabzon na kasar Turkiyya,a tazarar kilomita 300 a  saman rafin wannan yankin.
A shekarar 2010,babbar kungiyar Kiristanci ta Hasumiya mai fitila ta Girka ta shirya bikin addini a cocin na Sümela.
A kowace shekara dubun dubatan mutane daga ciki da wajen kasar Turkiyya ne ke yin cincirindo don kai ziyara cocin Sümela wanda mabiya addinin Kiristanci suka yi imani cewa tsarkakke ne.

Idan ku isa jami'ar Sümela wacce ke cike makil da tarihin daruruwan shekaru,zaku iya zagayawa a iyakokin Maçka don kashe kwakwarta idanunku ta hanyar kallon yanayi mai matukar daukar hankali na shahararren tafkin Uzungölü,gidan ajje kayayyakin tarihi na Ayasofiya,fadar shugabanci na marigayi,tsohon shugaban kasar Turkiyya,Mustafa Kemal Atatürk da dai sauran su.

Kazalika,kar ku sake ku bar yankin ba tare kun dandana dadadan girke-girken Bahar Rum,wadanda suka hada da kifin Alabalık wanda aka soya a man shanu da kuma wainar kwai na Kuymak wanda aka hada ta ta hanyar amfani da kwai,garin masara da kuma farin cikwi.
Sinyal…


 Labarai masu alaka