Ci gaban muhimman aiyukan da Hukumar TIKA ke gudanarwa a fadin duniya

A wannan makon zamu kammala sharhi akan ayyuka da manufofin hukumar TIKA bayan mun yi nuni ga ire-iren ayyukan da hukumar TIKA ke ci gaba da gudanarwa

Ci gaban muhimman aiyukan da Hukumar TIKA ke gudanarwa a fadin duniya

A cikin makonni uku da sunka gabata mun kawo muku daga cikin wasu muhimman ayyukan da Hukumar Haɗin Kai da Taimako ta Turkiyya TIKA ke gudanarwa a fadin duniya. A wannan makon zamu kammala sharhi akan ayyuka da manufofin hukumar TIKA bayan mun yi nuni ga ire-iren ayyukan da hukumar TIKA ke ci gaba da gudanarwa.

 

Ayyukan Hukumar TIKA daga gine-gine zuwa bunkasa ayyukan ma’aikatu

Daga shekarar 1995 kawo yanzu Hukumar TIKA ta gudanar da muhimman ayyuka a fadin duniya musanman a fannonin bunkasa tattalin arziki, al’adu da jin dadin al’umma. Kamar yadda muka sani hukumar na gudanar da wadannan ayyukan domin bunkasa da inganta rayuwar dan adam. Akan hakan ne ya sanya hukumar mayar da hankali da kara himma a fannin ilimi. Daga shekarar 1995 kawo yanzu hukumar ta gina makarantu, dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje, dakunan nazari da kuma raba kayan aiki ga jami’o’i.

A shekarar 2000 lokacin da yunkurin da ake yi na dunkulewar al'ummar duniya wuri guda watau globalisation ke ci gaba da shafar kasashe tun daga gabashi zuwa yammaci. A cikin wannan lokacin da kasashe masu magana da yâre daya ke bunkasa haka kuma hukumar TIKA ke ci gaba da bunkasa ayyukan da take yi a fadin duniya. Wannan hukumar mai muhimmanci ta kasar Turkiyya tana ci gaba da gudanar da muhimman ayyuka a kasashe masu hadaka da kasar Turkiyya.

A matsayar wata tubalar kasar Turkiyya wacce ke kokarin habbaka manufofin Turkiyya a fadin duniya, Hukumar TIKA ta taka rawar gani daga shekarar 2000 kawo yanzu. Daga cikin rawar da ta taka da bunkasar da ta yi shi ne fadada wuraren da take gudanar da ayyukanta a fadin kasa. Haka kuma a yayinda a shekarar 2002 take da ofisoshin gudanarwa guda 12 kachal, a shekarar 2011 yawan ofisoshin sun karu zuwa 25. A shekarar 2012 kuwa sun kai 33. A yau Hukumar Haddin Kai da Taimako ta kasar Turkiyya watau TIKA nada ofisoshi 61 a kasashe 59 tana kuma gudanar da ayyuka daban-daban a kasashe 150. A ko wace rana wannan hukumar na kara yawan ayyukan da take gudanarwa da kuma yawan kasashen da take gudanar dasu. Turkiyya na amfani da wannan muhimmiyar hukuma na ta domin samar da zaman lafiya a kasashen dake da kyakyawar hurda da ita.

Hukumar TIKA mai rajista a kasar Turkiyya na daya daga cikin hukumomin bayar da tallafi dake hadaka da kungiyoyi masu zaman kansu, jami’o’i da hukumomi domin gudanar da ayyuka iri daban-daban a fadin duniya.

A shekarar 2002 hukumar na bayar da tallafi da taimako na dala miliya 85, amma a shekarar 2017 wannan kasafin ya karu zuwa dala biliyan takwas da miliyan 120. A kan hakan ne Turkiyya ta kasance kasar da tafi ko wace kasa bayar da tallafi a fannin bunkasar rayuwar dan adam.

TIKA na hadaka da kasashen da ofisoshinta suke a kusan kasashe 150 a nahihoyi biyar domin samar da cibiyar ci gaba da bunkasar kasar. Ta hanyar TIKA, Turkiyya na koyar da ire-iren basirorinta ga kasashe tun daga Pasific, Asisya ta Tsakiya, Gabas ta Tsakiya, Afirka, Kasashen Balkan, Kafkasiya har izuwa Latin Amurka.

 

Masu sauraranmu a cikin wani sabon shirinmu mai taken “Hukumomin Ci Gaban Turkiyya”  muna fatar mu sake kasancewa daku a makon gobe.

Ku huta lafiyaLabarai masu alaka