Dutsen Sarki Lamarudu dake Turkiyya

Shin ko a wane sashen duniya aka fi yin kacibus da faduwar rana mafi kyau da ban sha'awa? Babu makawa, wannan tambaya ce da ka iya samun amsoshi da dama.

Dutsen Sarki Lamarudu dake Turkiyya

Shin ko a wane sashen duniya aka fi yin kacibus da faduwar rana mafi kyau da ban sha'awa? Babu makawa, wannan tambaya ce da ka iya samun amsoshi da dama.A jerin wadannan amasoshin kuma, akwai Dutsen Lamurudu da ke kudu masu gabashin Turkiyya.

Wannan tsaunin mai akalla tsawon kilomita dubu 2,150 na matukar daukar hankali illahirin masu yawon bude idon da suka isa dutsen Lamarudu a daidai lokaicin da rana ke gaf da ketowa a sararin samaniya don dusashe duhun dare.

Ko shakka babu, wannan ba shi ne abin daukar hankalin da tsaunin na Lamarudu ke da shi ba...A kokoluwar dutsen akwai katafaran gumaka na zamanin mulkin masarautar Komagene wadanda su ne ke fara yi wa maziyarta maraba da zuwa.Kawo yanzu babu wani wanda ya san yadda aka sassaka ko kuma kawo wadannan gumakan kan dutsen na Lamarudu.

Kamar yadda muka ambata a baya,a kokoluwar tsaunin Lamarudu akwai manya-manyan tuddai wadanda ke bin juna daga gabas zuwa yamma.Tsakanin wadannan tuddan akwai katafaran gumaka birjik masu girma mabambanta.Bayan an share shekaru bila adadin ana gudanar da bincike-bincike,an gano cewa wadannan gumakan na zamanin mulkin sarki Antichos na I na masarautar Komagene ne.

An kafa Komagene a shekarar 109 gabanin haifuwar Annabi Isa Allah ya yarda da shi, a matsayin 'yantacciyar Masarauta a yankin kudu maso gabashin Anatoliya,inda kabilu barkatai masu addinai da kuma al'adu mabambata suka yi zaman cude-ni-in-cude ka.

Sarakunan wannan masarautar sun gina haikaloli da kuma wuraren ibada a sassa daban-daban da zummar samar da zaman lafiya mai dorewa ta hanyar kara karfafa akalar da ke tsakanin su da ababen bautarsu.Gumakan Tsaunin Lamarudu na a sahun wadannan gine-ginen.Manya-manyan makabartu, gumaka da kuma allunan duwatsu da sarakunan Komagane suka sassaka da nufin sadaukar da su ga ababen bauta da kuma kakanninsu na a jerin ababen tarihin da kawo yanzu suka fi daukar hankali da kuma ban ta'ajibi a duk fadin duniya.

Ga wadanda ke bukatar kai ziyaraDutsen Lamarudu na yankin Adiyaman na Turkiyya,wanda hukumar bunkasa al'adu da kuma ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya,UNESCO ta saka a jerin muhimman wuraren tarihi na duniya, zi iya bi ta gundumar Kahta.

A duk lokacin da tafiyarku ta kai ku yankin,kar ku sake ku koma gida ba tare da kun ga kayayyakin tarihin masu dumbin yawa na tuddun Yenikale, gadar Cendere da kuma tsohon birnin Arsameia.

A gabar madatsar ruwan koramar Kahta, zaku iya dandana kifin korama,girke-girken gargajiya da kuma gane wa idanunku kyawawan kilisan wannan yankin, da dai sauran su .

Tsaunin Lamarudu na nan jiran ku !!!Labarai masu alaka