Ka'idojin da Hukumar TIKA ke amfani dasu yayin gudanar da ayyuka a fadin duniya

A halin yanzu dai Hukumar TIKA ta gudanar da ayyuka a fannin ilimi har 4,250 a ƙasashen Kolombiya, Falasɗin, Nijer, Makedoniya, Albeniya, Afganistan  da sauransu

Ka'idojin da Hukumar TIKA ke amfani dasu yayin gudanar da ayyuka a fadin duniya

Masu saurarenmu barkanmu da sake saduwa daku  a cikin sabon shirinmu “Hukumomin ci gaban Turkiyya”

A cikin wannan shirin namu a makon jiya mun fara bayyana muku ire-iren ayyukan da Hukumar Haɗin Kai da Taimako ta Turkiyya TIKA ke gudanarwa a faɗin duniya. A wannan makon zamu kuma ci gaba da zayyana muku muhimman ayyukan da hukumar ke ayyanarwa.

A halin yanzu dai Hukumar TIKA ta gudanar da ayyuka a fannin ilimi har 4,250 a ƙasashen Kolombiya, Falasɗin, Nijer, Makedoniya, Albeniya, Afganistan  da sauransu. Haka kuma a cikin shekaru biyar da sunka gabata hukumar tare da samar da sabbin tsarukan ilimi a waɗannan ƙasashe ta gina makarantu kusan dubu ɗaya da kuma sabonta wasu.

Hukumar TIKA tana kuma gudanar da ayyukan a fannonin noma da kiwo iri daban-daban domin kauda talauci, bunƙasa samun aiki ga mata, bunƙasa ƙauyuka da kuma samar da abinci. Makarantar gonar da hukumar ta gina a Mogadishu babban birnin Somaliya na ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da hukumar ke gudanarwa domin fa'idantuwar al'ummar Afirka akan dinbin arzikin da suke dashi. Haka kuma hukumar na karantar da matakan kauda hamada a makarantar. Ire-iren waɗannan ayyukan da Hukumar TIKA ke gudanarwa har a ƙasashen Balkan na daga cikin matakai masu dogon zangon da hukumar ke dauka domin kauda talauci da kuma samawa masu karamin ƙarfi kuɗaɗen shiga na dindindin.

Bugu da ƙari hukumar TIKA na gudanar da kataɓaren ayyukan noma na zamani da za'a rinƙa karantarwa akan harkokin noma da kiwo. Akan hakan ne hukumar ta gina cibiyar Zaitun ɗin Abasan a Gaza, cibiyar da zata bunƙasa tattalin arzikin yankin da samawa al'ummar yankin aiyuka daban daban. Daga shekarar 2017 kawo yanzu cibiyar ta samawa mutane musamman manoma 3,100 ayyukan yi a fannoni da dama. Daga shekarar 2016 cibiyar ta samar da ton 5,000 na Zaitun inda ta samawa gundumar Abasan kuɗaɗen shiga na dala 100 a kowace ton.

Sabuwar Tsarin TIKA: Tsarukan ci gaba irin na Ƙasar Turkiyya

TIKA, Ta fitar da wata sabuwar tsarin ci gaba irin na ƙasar Turkiyya dake gudanar da ayyuka bisa ga wadannan ƙa’idoji:

 

•           Fi sabilil Lahi                                                                                                  

•           Abokantaka

•           Bisa gaskiya

•           Kyautatawa ɗan Adam

•           Haɗin gwiwa a ayyuka

•           Haɗin gwiwa a samar da ilimi

•           Tallafawa juna

•           Warware matsaloli

 Labarai masu alaka