Labarin jaruma 'yar kasar Yaman Merwe mai ban tausayi

Shin ko ta yaya Turkiyya ke kawo ɗauki da ƙarfafa wadannan ɗaliban ? Labarin ƴan ƙasar Yaman Merwe ɗaya daga cikin amsoshin wannan tambayar ne.

Labarin jaruma 'yar kasar Yaman Merwe mai ban tausayi

Ƴar ƙasar Yaman Merwe

Sau da yawa mukan faɗaɗa wasu matsalolin da muka fuskanta waɗanda basu taka kara sun karya ba…..ldan muka damar da kanmu akan waɗannan matsalolin zamu sanya rayuwarmu, ƴan uwarmu da ƙasarmu cikin halin ƙaƙanikayi. Idan munka manta da wadannan matsaloli, munka kuma kalli yanayinmu da na ƙasarmu daga waje zai sanya mu cikin sukuni da bamu damar yin sharhi ingantacce. Akan hakan ne nike son in yaɗa wani labarin gaskiya, musamman yadda ƙasar Turkiyya ta aiyana shi.

 

Duk da irin halin da ƙasar Turkiyya ta samu kanta a ciki, tana ci gaba da kasancewa cibiyar neman ilimin dalibai daga ƙasashen waje. A lokacin da nake ɗalibi, Turkiyya bata ma kasance ƙasar da take iya ilimantar da kanta ba, amma a halin yanzu akwai kimanin ɗalibai daga ƙasashen waje dubu 150 waɗanda ke koyon Turkanci da neman ilimi iri daban-daban domin inganta rayuwarsu zuwa gaba. Wannan shinfida ce ga labarin da zan bayar. Ko wani dalibi nada nashi labarin daya kunshi nasara, matsala, cikas, ƙoƙari, ƙalubale da himma da yayi ko ya fuskanta a yayin ƙoƙarin samun gurbin karatu da tallafi a ƙasar Turkiyya. Shin ko ta yaya Turkiyya ke kawo ɗauki da ƙarfafa wadannan ɗaliban ? Labarin ƴan ƙasar Yaman Merwe ɗaya daga cikin amsoshin wannan tambayar ne.

 

Wannan sharhin Ferfesa Kudret BÜLBÜL ne shugaban kulliyar siyasa a jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt.

 

Yaman wacce ta yi iyaka da red sea, Gulf din Aden wacce kuma ke kan muhimmiyar taswira ta kasance tana fuskantar matsaloli da ƙalubale a ko wane ƙarni. Bisa ga lamarin da munka sani  Yaman na ɗaya daga cikin yankunan da anka fi samun wadanda sunka yi shahada a lokacin yunkurin kare Makka da Madinah. Haka kuma a lokacin yaƙin Çanakkale a ƙasar Turkiyya, ba mamaki a yankin Yaman ne anka fi kasancewa cikin zullumi da damuwa. A lokacin yaƙin Çanakkale al'umman Yaman  sun kasance cikin fargaba da damuwa game da halin da ake ciki.

 

Tafiyar neman sa'a …..

A shekarar 2014 kamar ko wacce matashiya ko matashi Merwe wacce ke zaune a babban birnin kasar Sana’a ta yanke hukuncin ficewa daga ƙasar domin bunkasa rayuwarta a wata ƙasar. A duk lokutan juyin mulki ba'a duba yanayin da kasa zata kasance a ciki balantana ma na matasa. Hakan ne dai irin halin da Yaman ta kasance a ciki.

A shekarar 2015 a lokacin da Yaman ta faɗa cikin halin jirinjiritsi Merwe ta zaɓi hanyar kuɓuta. A wannan lokaci ne ta miƙa takardunta ga Hukumar bayar da tallafin karatu ga ɗaliban ƙasashen waje ta ƙasar Turkiyya wato YTB. Kasancewar yadda aka dakatar da bayar da tallafin karatu ta Amurka wato Fulbright, na Jamus wato Daad da kuma na lngila wato Chevening sanadiyar yaƙin basasar Yaman, YTB hukumar tallafin karatun ƙasar Turkiyya ce kawai zaɓi tilo data ragewa Merwe da wasu matasan Yaman 150. Sun dai dauki dukkan matakan da zai sanya su zo Turkiyya su samu ilimi domin komawa ƙasarsu da niyyar sake gina ta.

A wannan niyyar, a ɗayan barayin akwai kyakkyawar fata a ɗayan barayin kuma akwai ƙalubale. Kasancewar yadda yaƙin basasa ya yi ƙamari a Yaman mafi yawancin ƙasashe sun mayar da aikin ofishin jakadancin su na ƙasar Yaman zuwa Jiddah dake ƙasar Saudiyya. Matsalolin tsaro sun sanya dakatar da tashi da saukar jiragen sama a Yaman. Domin zuwa ƙasar Turkiyya wadannan matasa na bukatar visa. Hanya daya tilo data rage musu domin zuwa Jiddah dake Saudiyya garin da ma'aikatan ofishin jakadancin Turkiyya na Yaman sunka koma ita ce ta mota. Sai dai kuma, akwai kungiyoyin dake kai hare-haren bama bamai da gudanar da rikice rikice iri daban daban a hanyar da zasu bi, sabili da haka bin hanyar mota hatsari ne kwaran gaske a garesu, babu tabbacin za'a iya bin hanyar mota daga Yaman zuwa Saudiyya a isa lafiya inma sun tafi ko sun isa iyakar Saudiyya babu tabbacin za'a bari su shiga ƙasar.

Matasan da sunka rasa mafita, sau da yawa sukan taru a wani guri dake babban birnin kasar Yaman wato Sana’a domin samawa kansu mafita. Daga bisani sunka yanke hukuncin baiwa wani matashi fasaport dinsu domin kaiwa Jiddah da zummar karɓa musu visar zuwa Turkiyya. Daga baya wannan matsashi, kasancewar yawan bama bamai da ake tayarwa a yankunan Yaman ya karaya ya kuma fasa.

Matasan sunyi iya kokarinsu har sunkai intaha. Sun rasa mafita. A daidai lokacin da suke daf da watsi da shirinsu na zuwa Turkiyya neman ilimi, wata macce mai kamar maza mai suna Merwe tace ita zata iya zuwa Jiddah domin karɓawa ƴan uwanta matasa visa daga ofishin jakadancin Turkiyya dake aiki a can.

Ƴan uwa da mahaifan Merwe sun kasance cikin damuwa akan wannan mataki da ta dauka har ma sun nemi da karta karɓi fasaport ɗin kowa ta tafi da nata kachal. Amma Merwe bata amince da hakan ba, ta tattara fasaport ɗin matasa kusan 90, wasu daga cikin waɗanda sunka samu nasarar tallafin karatun bata samesu ba, wasunsu kuma sunƙi bayar da fasaport dinsu domin suna hasashen koda ta samu isa iyakar Saudiyya ba za'a bari ta shiga ƙasar da kusan fasaport 100 ba a hannunta.

Jakadan Turkiyya dake Jiddah Fazlı Çorman ya yi farin ciki kwarai da gaske akan wannan kwarjinin na Merwe, lamarin da yake yawan maimaita wa a kalamansa na yau da kullum. Inda yake yawan nanata cewa, yarinyar ta saka kanta cikin hastari inda ta tattara fasaport ɗin matasa yan uwanta da suka samu nasarar tallafin karatu a Turkiyya kamarta, ta yi dakon fasaport dinsu daga Yaman har zuwa Jiddah domin karɓar visa.

Iyalen Merwe da ƴan uwanta ɗalibai da ta amshi fasaport ɗinsu sun dinga yi mata addu'a ba dare ba rana. Hakika wannan addu'ar da aka yi mata ya karɓu sabili da bata hadu da matsalar tasin bam ko hari ba a cikin kwanaki biyun da tayi akan hanyar ta zuwa Jiddah. Kasancewar ta ɗaliba ba'a gudanar da zurfin bincike akanta a duk guraren binciken da suka isa. Merwe ta isa kofar kwastan ɗin Yaman da misalin karfe 10 na safe amma ta tarad da layi mai tsawon gaske wanda a cikin rana ɗaya ma layi ba zai kawo gareta ba. A yayinda ta yi wa wani jami'i bayani ya taimaka mata inda tabi ta wata hanyar da ƙafa zuwa kofar kwastan ɗin Saudiyya.

 

“Ba zaki shiga ƙasar Saudiyya ba Muharrami ba”

Ta kuma fuskanci matsaloli a kofar kwastan ɗin ƙasar Saudiyya. A wannan ranar jami'an kwastan ɗin Saudiyya sun baiwa Merwe mamaki da tsoro inda suka bayyana mata cewa ki koma sai gobe. Ɗiya macce a cikin tsakiyar hamada ina zata? A cikin wannan yanayin Merwe ta aikawa jami'an ofishin jakadancin Turkiyya dake Jiddah saƙo ta fax, a wannan lokacin ne jami'an kwastan ɗin Saudiyya sunka bayyana cewar ba zasu bar Merwe ta shiga ƙasar Saudiyya babu Muharrami ko mijinta, ko babanta ko wani ɗan uwanta ba. Merwe dai duk da ta kasance tana bayyanin cewar ba aikin hajji zata ba, zata je karɓar visa ne kuma ba jimawa zata yi ba, domin zata dawo ne cikin kwanaki uku, sai da aka kwashe awanni tara anka bari ta wuce bayan ta samu Muharrami wanda ya aminta ya kuma rataɓa hannu.

 

Ma'aikatan ofishin jakadancin Turkiyya dake Jiddah sun yiwa Merwe babban tarbo inda sunka gudanar da aiki dare da rana domin kallama aiyukan visar.

Hakan dai ba shi ne ƙarshen wahalar Merwe ba, domin komawa Yaman na kuma tattare da hatsari tamkar zuwan. Akan hanyar su ta komawa sun tsallake rijiya da baya inda bam ya tashi daga wata motar bas a bisa wata gada dake gabansu. Bayan ɗaukar tsawon lokaci direban motar su Merwe na kutsa-fita a cikin hamada sun isa Sana’a babban birnin Yaman.

 

A halin yanzu Merwe na karatu a jami'ar Yıldırım Beyazıt. Haka ma sauran ɗaliban na karatu a jami'o'in Turkiyya daban daban da niyyar taimakawa ƙasar su zuwa gaba.

 

 Na sadaukar da wannan labarin ga waɗanda ke suka, har ma da ɓatanci, duk da irin damar da sunka samu, da ma wadanda ke ƴan soke-soke duk da basu je wata ƙasar sun gani ba, suna cewa “Ni bazan iya rayuwa a wannan ƙasar ba, gaba na nufa”

 

   Wannan sharhin ferfesa Kudret BÜLBÜL ne shugaban tsangayar Siyasa a jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt dake anan babban birnin ƙasar Turkiyya.Labarai masu alaka