Tsare-Tsaren Ilimi na Duniya Kashi na 1

Za mu gabatar da muku da sharhin Farfesa Kudret Bulbul, Shugaban TsangayarNazari Siyasaa Jami'ar Yildirim Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Turkiyya.

Tsare-Tsaren Ilimi na Duniya Kashi na 1

Dukannin mutane sun kasance suna rayuwa a doron duniya a matsayin wani katafaren iyalin bani Adama.Akwai ababe da dama da ke hada mu da kabilu bila’adadin mabanbanta wadanda suka zo wannan duniyar a zamani daya da mu.A duk lokacin da wani bala’i ya far wa wannan duniyar da muke ciki, ko dan wane kabila ne mu, ko mene addininmu,ko mene yarenmu, babu wanda zai tsira.İllahirinmu zai ya fasha.Kasancewar an halacce mu a karni, daya,ta sa akwai alaka ta musamman tsakanin mu da sauran kabilun wasu sassan duniya.Sani,al’ada da kuma lamurran yau da kullum sun kasance abubuwan da ke tasiri haikan wajen kullan hulda tsakanin mu da sauran kabilu ko kuma al’umomin duniya.Shin wannan tasiri ya fi girma a zamanin uwaye da kankanni,wadanda suka shude, ko kuma a wannan karnin da muke cike?

To bari, mu alakanta wannan lamarin da sani na zamani.”Ba a kasarmu kadai ba, a wasu sassan duniya manisanta da tamu kasar, akwai mutane masu kyau ko kuma mugun hali wadanda ka iya karkata akalar rayuwarmu.Miyagu na sanya tufafi cike makil da bama-bamai da nufin raba ku da rayuwa da kuma masoyanku.A wani sa’ilin kuma,muna kacibus da wasu mutane masu kyan hali, wadanda bamu taba sanin su ba, amma kuma, zasu matukar kawo muku sauki a rayuwarku, su kuma sake baku karfin gwiwar ci gaba da rayuwa.

Shi yasa ilimi ruwan dare ne gama duniya,kana abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke saurin yaduwa.Masu kyau da mugun hali na wata kasa na iya haifar da babban tasiri kan lamurran wata kasa ta daban.

Shin mene matsayinmu a duniya a fannin ilimin ?

Babu makawa , akwai nasori da dama da muka cimmawa.Amma,a sharhinmu na yau, zamu ambaci matsalolin da ke tattare da ilimin wannan karnin da muke ciki.

Idan muka kalli Yammacin duniya,a makarantun Amurka wadanda a yau suka zama tamkar sansanonin soja, kisan kai ya fi na sauran kasashen duniya sau biyu.Yawancin dalibai na kashe abokansu, manya,yara da tsaffi.Yara na tsuduma lalata,a lokacin kuruciya kuma,suna wantagaririya a titi,caca,kora barasa,aikata miyagun aiyuka da kuma datse alakar da ke tsanin su da iyayensu ta yadda ko bukukuwan sallah ma, ba za ta taba hada fuskokinsu ba.

A Yammacin duniya ma,abin bai sha bamban ba.Ko ma lamirin bai kamari ba kamar a Amurka, a Turai ba a bai wa yara cikakken shirin gwagwarmaya da lamurra da ke wakana  rayuwarsu,ba su da ‘yancin fadin albarkacin bakinsu ko kuma bayyana tunaninsu.Yawancin lokuta, harda ce ake kowa musu bakatatan,ana ba su horon da ba zai taba amfanar su ba a rayuwarsu ta yau da kullum.

A duniyar Islama kuma, rashin wata alaka tsakanin horon da ke bayarwa da kuma rayuwar,wata babbar matsala ce da Aliya Izzet Begoviç ya nuna da yatsa.

Idan ilimi ko rashin sa na iya yin tasiri kan mokamar kowace kasa, to kamata yayi a yi muwafaka na bai-daya kan irin horon da za a bai wa al’uma,wanda ya kamata a ce bai da wata alaka da kowane irin addini,yare,tunani,ra’ayi da kuma kalar fata,kabila ko kuma makamancin haka. Akasin haka na nuna cewa, iyalin bani adama na gaf da halaka.

Don samar da dauwamammiyar zaman lafiya, kwanciyar hakali da walwala a wannan duniyar,tilas ne ilimi ya zama a sahun gaba na muhimman siyasoshin da  ya kamata mu sa gaba.Garin samar da wadannan siyasoshin, muna iya fara tambayar kawunanmu kan manufar da muka sa gaba.

Kamata yayi a ce manufar ilimi ita ce bai mutum damar magance matsalolin da zai fuskanta a rayuwa a sauwake.A hakikannnin gaskiya,irin tsarin ilimin da muke bukata na da alaka ne da irin yadda muke fuskantar rayuwa.Falsafar da ke dangance iliminmu wani bangare na manufar da muka sa gaba a rayuwa.Ya ci ace ilimi ya taimaka wajen gina wata duniya,wacce ke  da marasa shiri kalilan ne,miyagu cikin cokali,inda aka fi martaba ra’ayoyin mutane mabambanta,jama’a kuma suka rungumi adalci.Idan aka ce ilimi, ba wai ana nufin boko kuma tsarin ilimin nasara.Shi yasa makaranta, daya daga cikin makamai ne na cimmawa sani,ba wai hanya daya tak ba ce ta samun ilimi.

Idan manufar mutanen duniya daya ce, kana bukatar dukanninsu ita ce samar da tsarin ilimi,to kamata ya yi mu rungumi ilimin da zai taimaka wajen kare hakokkin kabilu marasa rinjaye da tabbatar da kyaukyawar makoma ga kowa. Shin ko wadanne siyasoshi wadannan ?

1. Tsarin ilimi mai da’awar adalci

Ko a wane zamani muke rayuwa (Jahiliyya,kan-tawaye,wayewa ko kuma makamancin haka) ,komai yadda muka gabatar kanmu mu gabatar,kamata yayi manufar ilimi ta zamo adalaci. Kamar yadda sahibin manzon Allah, Omar bin Khattab ya ce,”Adalci gimshiki ne mulki”.Masanain kasar Jamus, Kant kuma cewa ya yi: “ Idan adalci ya gushe,babu wata darajar da ta yi rayuwar bil adama saura”.Saboda sai da adalci ke iya kare hakki da kuma ‘yanci.Ko da yake ra’ayi kan ainahin ma’anar adalci ya sha bamban daga wannan kabila ya zuwa waccar.Amma gimshikai adalci a kowane kusan daya ne.Dukannin addinai,tunace-tunace,akidoji da kuma ra’ayoyi na wannan duniyar,sun haramta sata,kisa,tara kudu ta hanyar haram,ko kuma kulla mummunar mu’amala.

Shi yasa, a firamari,sakandari har ma da jami’a, abu na farko da yakamata a ce an fara koya wa dalibai shi ne, tara halaliya ta hanyar aiki tukuru, ba wai rungumar haram ba don cimma buri.Sanin kowa ne, kishiyar adalci,zalunci ne.Mu dan  yi la’akari da ya cewa,kowa ya dukufa neman haram a makamance ba tare ya bi doka da oda ba.Shin ko muna iya hasashen irin bala’in da hakan zai haifar ?

Ana iya cike gurbin ragowar sanin  da muka rasa a makarantu,wanda ke nasaba da gani,ji da kuma aiki, daga baya.Amma ba zamu taba iya cike gurbin adalcin da ba mu tabbatar ba a tsawon rayuwar da muka yi a makaranta.

Adalci,ba lamari ba ne da za a ce an samar da shi yayin da ake bai wa dalibai ilimi.Kamata ya yi a tabbatar da shi a aikace a halayya da rayuwar yau da kullum ta malamai masu bada horo.Wato maimakon a tabbatar da ilimi a rubuce ko a fatar baki ta yadda dalibai zasu haddashi ba tare sun san ma’ana ko kuma muhimmancinsa, kamata ya yi a cusa musu shi a kwakwalen da tunaninsu.Tilas ne, a guje wa rashin adalci,wanda ke haifar da zaluncin da dumbin matsalolin da ke nasaba da shi.

2. Tsarin ilimi mai haddasa kyan hange da tunani

Kamata ya yi tsarin ilimi ya kasance ya samar mutane masu kyaun ruhi,zuciya da tunani.A ko ina muka waiwaya,sai mu ga matasa wadanda tun a kuruciyrsu ba sa ganin komai fa ce rashin nasara da bakin tunanin.Matasa wadanda tuni suka yanke kauna daga rayuwarsu,kana wadanda ba su yarda da kawunansu.Shin wannan wacce irin rayuwa ce? Shin  wace irin makoma ce za iya ginawa da irin wannan bakin tunanin? Kamata ya yi kowa ya dinka hange da kuma ganin kyaukyawan abu.Duk da cewa “Kyau” da “Rashin sa” ababe ne da mana’arsu ke sauyawa daga al’ada da kuma addinin wannan sashen duniyar ya zuwa wancan.Ko da yake a yau, akwai musababbai da dama da ke haddasa wannan lamarin.Saboda ba ruwan kowa da samar da mutanen nagari.A kulli yaumin, kamata ya yi,mu kallo,gani da kuma tunanin mai kyau,don samar da kyaukyawar rayuwa da kuma kulla sahihiyar alaka da mutanen da tare da mu.Yin tunanin mai kyau,na da mtaukar muhimmanci,kana yana gaba da adalci.

Mu hadu a mako mai zuwa dan cigaban wannan shirinLabarai masu alaka