Musulman Indiya

Zamu gabatar muku da sharhin farfesa Küdret Bülbül Shugaban tsangayar nazarin Siyasa a Jami'ar Yıldırım Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

Musulman Indiya

Matsalolin Kasashen Duniya: 36 

A wani littafinsa mai suna “Yanayin Zamanin Kan-tawaye” da ya wallafa,masanin ilimin zamantakewa na kasar Burtaniya David Harvey,ya gabatar da karninmu na yau, a matsayin zamanin dunkulewar tazara da na lokaci.Yayin da matakan akidar “Duniya a tafin Hannu”,wato Golbalization da muka cim ma a wannan zamanin, ke ci gaba da kusantar tazarori masu nisan gaske, a wani sa’in kuma, suna nesanta wurare makusanta.Suna iya taimkawa wajen manta tarihin bai-daya na al’umomin kasashe mabambanta.A shirinmu na wannan makon, zamu tabo batun Musulman Indiya.Sanin kowane, Indiya daban ce da kasar Mekziko a fannin zamantakewa.Shin tun fil azal, haka lamarin ya kasance a tarihance ?

Mantaccen tarihin Islama na kasar Indiya

Dakta Omar Anas,shugaban cibiyar bincike ta Mashreq da ke New Delhi, babban birnin kasar Indiya,kana bakon malami a tsangayar ilimin zamantakewa na Jami’ar Yıldırım Beyazit na birnin Ankara,wanda tashar talabijin TRT da Rediyon Muryar Turkiyya TSR suka karbi bakwancin sa a shirin Çeşmi Cam, ya ce Musulunci ya isa kasar Indiya ta hanyoyi guda uku.

Hanya ta farko ita ce, kasuwanci, kamar a kasar Indonesia,inda Islam ya dinka yaduwa ta hanyar saye-da-sayarwa.Dukannin wadannan ke yin aikinsu kan gaskiya, na ci gaba da samun yardar jama’ar nahiyar,wanda hakan ya yi tasiri haikan  wajen yada wannan addinin.

Hanya ta biyu ita ce, tasirin da Sufiyawan tsakiyar Asiya suka yi kan Indiya.Dakta Anas, ya ce kowa ya san Maulana Jalaluddeen Rumi a nahiyar.Kazalika ya jaddada cewa,Musulman Indiya, musamman ma Sufiyawa, na ziyatar birnin Konya a duk lokacin da suka zo Turkiyya.Bugu da kari, Maulana na iya zama wata babbar gada tsakanin kasashen Indiya da Turkiyya.Idan muka dubi rayuwarsa,ko shakka babu, zamu ga cewa, daya kafarsa na Indiya yayin dayar kuma, na a yankin Anatoliya,inda tarihi da kuma sakonsa suka ratsa karnoni bila-adadin.A kulli yaumin,kalamansa na ci gaba da hada kan mutanen kasashe da kuma sassa daban-daban na duniya a tsawon daruruwan shekaru.

Hanya ta uku ita ce, mulkin Musulunci wanda ya aka share karnoni da daman ana yin sa a Indiya.Shugabanni Musulmai Turkawa sun fara tasiri kan kasar a wajejen shekarar 1000.Kamar yadda da aka sani, daulolin Musulunci na Usmaniyya da na Andalusiyya sun nuna karamci, jin-kai da kuma kauna a mulkinsu,inda suke rayuwar cude-ni-in-cude-ka da al’adun al’umomin yankin da suke iko.

Yankunan Indiya na da manyan mu’addibai kamar su marubucin littafin “Mektubat” Imam Rabbani (1564-1624),matuburin “Hujjatullahil Balik” Shah Waliyullah Dehlawi (102-1662),marubucin littafin “Shin kowane irin asara duniya ta yi yayin da Daulolin Musulunci suka ja da baya ?”,Abu Hasan al Nadwi (1914-1999) da dai sauran su.

Bayan mulkin mallakar Turawan Ingila,Musulunci ya dinka ja da baya a Indiya,har sai ta kai kowa ya fara jahiltar sa,inda daga bisani kuma,aka mance da shi ga baki daya.Muna iya cewa, siyasoshin mulkin mallaka Burtaniya da kuma gwagwarmayar samar da zaunannen tarihi da ‘yantattun al’adu da Pakistan da Bangaladesh suka yi da zummar ballewa daga Indiya, don cin gashin kansu,na daga cikin dalilan da suka haifar da wannan lamarin.

A yau Indiya mai sama da Musulmai milyan 200 na a matsayin ta 2 a jerin kasashen da suka fi yawan mabiya addinin Musulunci,inda Indonesia ke a sahun gaba.Idan muka kalli yankin Indiya, zamu ga cewa, akwai akalla Musulmai milyan 600, yayin da al’umar Indiya ga baki dayanta biliyan 1 ne da milyan 300.Halin da Musulman Indiya ke ciki a yau,abu ne da ke bakanta rai sosai.Ana ci gaba da kai wa Musulman yankin Assam hare-haren kyama da na ta’addanci a kulli yaumin.

Shekaru 700 na mulkin sarakunan Musulmai Turkawa

Tun daga wajejen shekarar 1000 ya zuwa ta 1857, sarakunan Musulmai Turkawa ne suka ci gaba da gundanar da mulkinsu a yankin Indiya.Wannan mulkin ya fara da kabilun Turkawa na  Gazniyawa.Sarakunan da suka fi shahara su ne,Sarkin kabilar Turkawa ta Çağatay, Babür shah da dansa Cihangir Shah wanda suka kafa daular Babür.Daular Babür ya gushe a shekarar 1857,a lokacin da Turkawan Ingila suka yi galaba kan Shah na karshe na daular Babür, Bahadır shah,a wani yaki da suka fafata.Sanin kowa ne, akwai lakar kud-da–kud tsakanin sarakunan Musulmai Turkawa na daular Usmaniyya da takwarorinsu na Indiya.Wasu daga cikin gimbiyoyin Daular Usmaniyya,bayan an tirsasa su yin hijira da karfi da yaji daga kasarsu ta ainahi,sun auri yarimomin Indiya.

Inda Ingila ta mallaki Indiya tun da wuri ,Musulmai ko su gano Amurka?

A kasar Indiya ta yau, akwai harsunan hukuma 18,jihohi 22, da kuma akalla yaruka 400.Watakil Indiya ta kasance kasar da ta fi arzikin addini,harshe,al’ada da na jama’a mabambanta a duk fadin duniya.Ko shakka babu, bunkasar wannan arzikin ya zuwa zamanin da muke ciki,na nuna babban tasiri na salon mulkin sarakunan Musulmai a tsawon karnoni da dama.Saboda wadannan shugabannin,mamaikon su yi wa al’adu, harsuna da kuma addinan da suka tarar a matsayin ababen kyama wadanda ya kamata a kawar don maye gurbinsu da wasu,sun kalle su a matsayin wani bangare na wayewarsu.Sarakunan Usmaniyya sun gudanar da mulkinsu kamar takwarorinsu Larabawa a Andalusiyya.Shi yasa a lokacin da mulki ya kubuce wa Musulmai,illahirin harsuna,al’adu da kuma addinai suka ci gaba da kasancewa kamar a da.Yayin da kasashen Balkan babu wanda ya iya magana da Turkanci, a Andalusiyya kuma, babu mutum daya da ke iya tada bakin Larabci,a yau Ingilishi ya zama harshen hukuma a kasashen Indiya,Pakistan da kuma Bangaladesh.A Amurka kuma, inda lamarin ya fi tsamari,ana ci gaba da gwagwarmayar kare harshe, addini da kuma al’adun al’umomin ainahi, tamkar jinsin tsuntsayen “Ibis” da ke gaf da gushewa daga doron duniya.

Shi yasa dole ne irin wannan tambayar ta dinka gittawa a kwakwalwar mutum: Shin ko me zai faru,inda Ingilawa sun mallaki Indiya a wajejen shekarar 1400,maimakon a shekarar 1800 ?

Watakil kamar a Amurka,Indiya ma, za ta kasance a jerin kasashen da aka tirsasa wa jama’arsu rungumar addini da kuma harshen “Masu farar fata”,share al’adunsu ga baki daya don maye gurbin su da na Turawan Yamma.

Ko kuma, bari mu yi hasashen akasin hakan,wato Shin ko me zai faru,inda Musulmai ne suka fara gano Amurka,ba wai Turawa ba? Shin yaya yanayin Amurka zai kasance a yau ? Shin ko al’adu, harsuna da kuma addinan al’umomin ainahi na Amurka,wadanda suka hada da Astec,Inca,Maya da dai sauran za su gushe, ko kuma wadannan kabilun ne, za su ja akalar mulkin Amurka a yau ?

Bayan mulkin mallakar Turawan Ingila a yankin Indiya,jama’a sun rungumi akidar Burtaniya da ta Turawan Yamma, yayin da aka raba kasar uku,Indiya,pakistan da kuma Bangaladesh.Kawo yanzu ana ci gaba da cece-kuce kan musababbin wannan lamarin,inda aka dasa ayar tambayar kamar haka : “Shin rarrabuwar Indiya,sakamako ne na siyasar “Raba kawuna don ka ji dadin mallaka” na kasar Burtaniya mai akidar jari hujja, ko kuma yankan kauna ne, na Musulman da aka dinka gasawa aya a hannu?”.

Inda Indiya ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa daya tilo, da a yau wadannan kasashen ba zasu ci gaba da kyamar junan su ba,haka zalika matakan da yawan Musulman da ke kasar za su dauka, za su yi matukar tasiri a siyasar nahiyar Asiya,wanda hakan zai iya zama silar samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Musulman Indiya da Yakin Kurtuluş na Turkiyya

A yakin duniya na farko a lokacin da Ingilawa suka fara kai wa yankunan daular  Usmaniyya farmakai,Musulman Indiya sun nuna bacin ransu sosai,duk da yake su ma, sun kasance karkashin mulkin mallakar Burtaniya.A fahimtarsu, idan har Daular Usmaniyya ta fada hannun Ingila, to babu makawa,mullkin mallakar karsarsu za ta zurfafa kana ba zasu taba tammahar cim ma burinsu na kubuta daga hannun Turawa.Don tallafa wa Daular Usmaniyya, Cinnah da Gandhi ma,sun hada karfi da karfe da sauran al’umar Musulmai don fara kaddamar da “Farmakan Kare Halifanci”.Wadanda suka jagoranci wannan fafutukar,sun gana da shugabannin mulkin mallakar Ingila na wancan lokacin.A Yakin Kwato‘Yancin-kai na Kurtuluş na Turkiyya, Musulman Indiya sun tara makudan kudade don tallafa wa Turkawa da ke yaki da Turawan Yamma.

Bari mu waiwayi akidar “Duniya a tafin Hannun”, wato Globalisation, wanda muka bude shirinmu da ita.Kamar yadda muke ce a baya.Yayin da a daya gefe akidar “Duniya a tafin Hannu” ke ci gaba da kusantar tazarori masu nisan gaske, a wani sa’in kuma, yana nesanta wurare makusanta.Haka zalika, yana iya taimkawa wajen manta tarihin bai-daya na al’umomi mabambanta.Fatar Turkiyya a yanzu haka ita ce, karfafa ingantacciyar hulda “Mai gaba-dubu” da daya daga cikin manyan kasashe na karni na 21,wato Indiya.Labarai masu alaka