Ingantaccen tunani ko hangen nesa? Wanne ne ya fi ?

Zamu gabatar muku da sharhin farfesa Kudret Bulbul Shugaban tsangayar nazarin Siyasa a Jami'ar Yıldırım Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

Ingantaccen tunani ko hangen nesa? Wanne ne ya fi ?

Matsalolin Kasashen Duniya: 35

A makalolinmu na baya, mun sanar da cewa bai kamata ba mun dinka rungumar tunanin rashin nasara a duk lokutan da muka ci karo da sabbin ababe,ra’ayoyi da kuma matsaloli,don waiwayar ababen da suka tabawa wakana a baya,kallan yanayin da muke cikinsa,don magance komai cikin ruwan sanyi da hikima. Amma ayar tambaya  a nan ita ce, shin ra’ayoyin da aka gina kan ginshikai nagari, su kadai na iya iya warware dukannin matsalolin duniya ? Shin akwai yiwuwar hakarmu ta ci ma ruwa  ?

Zamu gabatar muku da sharhin farfesa Kudret Bülbül Shugaban tsangayar nazarin Siyasa a Jami'ar Yıldırım Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

Muna iya cewa, gina ra’ayi kan ginshiki nagari da kuma hangen nesa,su ne hanyoyin mafi muhimmanci wajen warware bakin zaren kowace matsala ko kuma cimma kowace irin manufa.Duk yadda zamu nuna kuzari, idan har hanyar da muka bi ba ita ce ya kamata a ce mun dauka ba,to babu ta yadda za a yi mu cimma manufofin da muka sa gaba.A daya gefe kuma, rashin sanin mece manufarmu shi ma, babban kuskure ne kamar yadda daukar hanyar da bata dace ba ya kasance ba daidai ba.Duk jirgin ruwan da bai san inda ya dosa ba, babu wata iskar da za ta taimaka masa.Shi yasa batun neman gina ra’ayi kan gimshiki nagari,a duk lokutan da mu yi kacibus da sabbin ababe, matsaloli ko kuma tunace-tunace,magana ce marar tushe.Amma, shin hawa kan wannan tafarkin kawai na iya sa hanyarmu ta bille ? Dole ne mu zurfafa tunani.Saboda a yawancin lokuta, ana zaton cewa sanin da aka yi amfani da shi wajen haifar da kace-nace,isasshe ne.Ana matukar bai wa cece-kucen da wasu gungun mutane masu zaman kashe wando ke yi a kusurwowin gidajen shan kofi, muhimmanci sosai. Shin a duniyar Islama,ana iya magance dukannin matsaloli ta hanyar yin tunani mai kyau? Wane muhimmanci tunani ke da shi?

Ko shakka babu tunace-tunace na matukar muhimmanci.Abubuwan da suka fi kawo sauye-sauye a tsawon karnoni da dama a tarihin bil adama, su ne tunace-tunace.Amma wadannan tunace-tunace, su ne wadanda aka tabbatar da su a aikace, ba wai wadanda suka ci gaba da kasancewa a fatar baki kawai ba,wato wadanda ba a taba yin aiki da su ba.Wadannan tunace-tunacen su ne ke gina rayuwarmu, ba wai wadanda suka tsaya a kwakwalenmu kawai ba.Shin mene amfanin tunaninmu,ko da mun gina shi kan ginshiki nagari,idan har ba zamu taba amfani da shi ba, don kawo wani sauyi a rayuwarmu da ta illahirin jama’ar al’umarmu ba? Akwai yiwuwar tunaninmu ya zama ingantacce,ama zamu iya ci gaba da zama a inda muka saba zama ko kwana a inda muka saba kwana,wato ba gaba ba baya.Shi yasa kamata ya yi maimakon mu dinka yi wa kamnu karya ta hanyar tunanin cewa, cece-kucen da wasu da ke kiran kansu kwararru ke yi ba tare da sun tabbatar da su a aikace ba, ko kuma suke ganin cewa ba ta yadda za a yi su aikatu, kamata ya yi mu tashi tsaye kan kafafunmu don kawo sauyi.

A daga gefe kuma, abin da kamar wuya a ce tunanin mutumin da ya ware kansa daga sauran jama’a ba tare da ya cakudu da duniya ba, ya iya zama ingantacce.Wannan wani batu ne da kawo yanzu ake ci gaba da cece-kuce kan sa.A yawancin lokuta, irin wannan tunanin wanda bai ginu ba kan rayuwar yau da kullum, na iya haifar da dumbin matsaloli.Da wuya mu waiwayi tarihin bil adama ba tare bakin ciki ya lullube zukatanmu ba, saboda cike yake makil da irin wadannan mishkilolin.Babu makawa, tsaida rayuwa ko kuma ware kanmu daga ita da nufin gina wani ingantaccen tunani wanda zai iya warware dukannin matsalolin da duniya ta kunsa a lokaci daya,abu ne da ka iya haifar da manyan masifofi.Shi ya sa tunani ba zai taba zama nagari ba, har sai an gina shi a tsawon rayuwa duba da ababen da muka dinka fuskanta nan da can.Addinin Musulunci ma, a haka ya ginu.Saboda bai kammalu a daya lokaci ba.Ya dinka yaduwa ne sannu a hankali a tsawon zamaninnika,inda yawancin lokuta ya dinka cigaba da kammaluwa duba da sabbin ababen da suka afku a tarihin bil adama.

A yau, duk da ababen da muka ambata a baya,bamu kasance kwata-kwata a cikin duhun jahilci ba, game da hanyar da ya kamata mu bi, aikin da ya ci a ce mun yi ko kuma halin da ya kamata a ce mun nuna.Saboda mafi yawancin dabaru, kowa ya san da su.A yau, daya daga cikin mafi girman matsalolinmu shi ne, yadda maganganunmu suka yi hannu riga da halayyarmu a karara da kuma zuba na mujiya da muke ci gaba da yi ba tare mun yi wani abun a zo a gani ba, duk da muhimmancin da maganganunmu da ke shi.Sanin kowa ne, rayuwa, imani ne da jihadi.Jihadi na nufin aiki tukuru,bai wa tunani ruhi ta hanyar tabbatar da shi a aikace,mujadala ce, kuzari ne da kokari.Daya daga cikin jihadoji,shi ne wanda aka ke yinsa a tafarkin addini,wanda a yau,kusan ba a faye bukatar sa ba.Abinda da muke bukata a yau shi ne,nuna kuzari wajen yin aiki da tunani mai kyau, nuna hali nagari da kuma yin aikin tukuru wajen tabbatar gaskiya,adalci da kuma duk wasu aiyuka da manufofi  masu kyau a doron duniya.Abin nufi a nan shi,ba zamu iya dogaro da kyan hali da manufa ba kawai.Saboda ko ana da kyau dole aka kara da wanka,wato dole ne mun dinka mujadala ba dare ba rana a dukannin fannonin rayuwa.

Idan muka koma kan su’alin da muka yi a farko shirinmu, ko shakka babu, zamu iya cewa, kin gina ra’ayi ko tunani kan ginshiki nagari,tamkar yin tuwa ne babu albasa.Saboda,kin yin haka na iya karkata alkiblarmu daga manufofin da muka sa gaba don tsunduma mu cikin manyan bala’o’i.Kin gina tunanin kan ingantaccen ginshiki, na iya halaka aniya ko kuma ra’ayin mutum komai kyansa.Amma duk da haka,ko da mun gina ra’ayinmu kan kyaukyawan ginshiki ma, ma zamu taba tsira ba.Akwai yiwuwar wannan tafarki ne da ka iya sarrafa kansa.A duk lokacin da aka hau shi,sai ya dinka tafiyar da komai karan kansa har sai ya cimma manufarsa.Domin komai kyan aniya ba za ta taba haifar da kyaukyawan sakamako ba, har sai ta aikatu.Aniya ita ce farkon komai.Idan muna son mu ga sakamakon, dole mu dinka gudanar aiyukan da suka ginu kan ginshikai nagari wadanda kuma ka iya taimaka mana wajen tabbatar da aniyarmu a aikace.

Shin a yau wadanne ne halaye ko kuma tunace-tunacenmu, wadanda ke hana mu gina tunaninmu kan ginshikai nagari ne, ya kamata a ce mun sauya?Shin akwai yiwuwar mu magance dukannin matsalolinmu ta hanyar fakewa da laifukan na kusa da mu, duk da yake a yawancin lokuta bamu ganin laifukanmu sai na wasu ? Shin idan bamu tashi tsaye ba don kunna kyandar,yin Allah wadai da duhu na iya kawo mana haske ? Wadannan su ne tambayoyin da za mu yi kokarin bada amsoshinsu a makalarmu ta gaba.Labarai masu alaka