Ba rungumar tunanin rashin nasara ba, kusanci cikin hikima

Sharhin Farfesa Kudret Bulbul Shugaban tsangayar nazarin Siyasa a Jami'ar Yıldırım Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

Ba rungumar tunanin rashin nasara ba, kusanci cikin hikima

Matsalolin Kasashen Duniya: 33

A makwannin da suka gabata, mun zanta kan ra’ayoyi uku game da Yamma da masanan duniyar Islama na zamanin Daular Usmaniya suka gabatar, wadanda suka hada da “Mika Wuya”,“Yin Watsi” da kuma “Nuna Hikima”.

Babu wata alaka tsakanin ra’ayoyi biyu na farko, hasali ma za a iya musu kallon kishiyoyin juna.Ko da yake a wani bangaren, ana iya cewa, akwai wata kankanuwar dangantaka da ke tsakanin su.Ga masu neman mafakan da ke rayuwa a yammacin duniya,wadannan ra’ayoyin biyu,wadanda Musulmai suka runguma, na iya maida su saniyar ware.Halayyar da masu ra’ayin “Mika Wuya”,wadanda tuni suka salwance tare da juya wa al’adu da kuma tarihinsu baya ga baki daya,na iya zama ummal’aba’isar wariyar da ake nuna wa wasu gungun masu ra’ayin “Yin Watsi” da ke Yamma.Akasin haka ma, na iya zama gaskiya,wato abin nufi a nan shi ne,masu ra’ayin “Yin Watsi” da wayewar Turai,wadanda suka juya wa ra’ayoyi, akidoji da kuma dokokin Yamma baya, na iya haifar da kalubale ga wasu gungun masu “Mika Wuya”.A gefe daya kuma, da yake ra’ayin “Mika Wuya” da na “Yin Watsi” basu kasance wasu halaye wadanda aka a haifi mutum da su ba,ana iya a wayi gari babu su babu dalilinsu,saboda ba zasu ci gaba da zama a dunkule a zukanta wadanda suka rungume su ba, a yau.Da yake dukannin ra’ayoyin biyu sun kasance tsaurara, akwai yiwuwar wannan wata dabi’a ce wacce mutane ke yin amfani da ita, don ware kansu daga sauran makamantansu ko kuma gwagwarmayar samun matsayin da ya dace da su a zamantakewarsu ta yau da kullum.A duk lokacin ba su yi wa wadannan ra’ayoyin biyu makwauniyar runguma ba,har ta kai ga zama halayarsu,muna iya yin la’akari da sauye-sauyen ra’ayoyi daga wannan shiyya ya zuwa wancan,wato daga ra'ayin “Mika Wuya” zuwa “Yin Watsi”, ko kuma daga alkiblar “Yin Watsi” zuwa ta “Mika Wuya”.Kadan kenan daga cikin dalilan  da suka sa wasu daga  cikin “Musulman” da ke rayuwa a Yamma, wadanda suka juya wa addini baya, masu aiki a gidajen kora barasa, masu kwankwatar giya,kana suka nasarance daga jiki har ruhi,suke cincirindo don zuwa kungiyar ta’adda ta DAESH.Daga masu ra’ayin “Mika Wuya” har ya zuwa masu “Yin Watsi",babu ko daya na kwarai a cikin su.Saboda ba zasu taba amfanar kasashen da suke rayuwa a cikin su da komai ba, kana basu da wata makoma.

Ba rungumar tunanin rashin nasara ba,kusanci cikin hikima

A yau a Yamma,idan da akwai wani ra’ayi da ake iya na’am da shi, shi ne na nuna “Hikima” kamar yadda daya daga cikin jiga-jigan daular Usmaniya,Said Halil Pasha ya nuna , ba wai  “Mika Wuya” ko kuma “Yin Watsi” ba.A yakin duniya na farko,a tsakiyar wannan rashin tausayi da kazamar fafatawar, duk da irin yadda duniya ta dinka tofin Allah tsine kan Yamma, Halim Pasha ya nuna hikimar da ko a yau da wuya za a samu wani masanin da zai nuna shi.Wannan wani lamari ne da yakamata a jaddada shi kwarai da gaske.A kasashen Yamma, ainahin tushen bullowar ra’ayoyin “Mika Wuya” da na “Yin Watsi”,na da nasaba ne da yadda mutane ke rayuwa a zamantekwarsu ta yau da kullum.Bugu da kari, a yawancin lokuta,an danganta wadannan ra’ayoyin da a’aldu da kuma addinan masu rungumar su.Idan aka kalli matsalar ta bangaren Musulunci,addinin da ya tanadar da dukkanin hanyoyin warware matsalolin mutane daga kakanmu,Adam alaihis salam ya zuwa karshen duniya,ba zai taba ginuwa kan wani ra’ayi da ka iya zama kishiyarsa ba .Saboda,Islam,tsarin rayuwa ne da ya dogara kan wata makomar da babu wanda ke da tabbaci a kanta.Musulunci da karan kansa,garkuwa ce,gini ne mai nagartaccen ginshiki.Gina ra’ayi kan lamirin da kuke suka,tamkar zama musabbabi ko kuma cibiyar wannan abin kyamar ne.Shi yasa ka’idar shiga ta farko ta Musulunci ke farawa da kalmar shahada,wato harafin “La”,wanda ke yin watsi da duk wani gurbataccen imani.Zamantakewar Mu’munai kuma, ta ginu kan Ilimi.An fada cewa, a nemi ilimi, ko da ya kasance a kasar Sin.Shin mene ilimi ? Fasaha, kimiyya,sani, amfani,alkiblar rayuwa, tsari su ake kira da ilimi.

Game da wannan batun, rayuwar da mafificin halitta, Annabi Muhammad Tsira da Aminci Allah su tabbata a gare shi,ya yi da jahilan  Makka,shi ne mafificin misali a gare mu.Saboda a wancan zamanin, mutanen Makka sun cim ma koluluwar jahilci.Mu’amalar Manzon Tsira da wadannan mutanen, na iya zama wata taskar sanin yakamata ga wadanda a yau ke rayuwa a kasashen da jahilici da rashin imani ba su yi tsamari sosai ba.An tabbatar da cewa, Annabi ya kulla huldoji iri uku da jahilar al’umar Makka.Wasu daga cikin lamurransa daya suke da na jahilan Makkah.Alal misali,idan muka kalli ta bangaren tufafi da barin geme, babu abinda ya bambanta shi da su.Manzon Allah bai yi yunkurin kawo wasu sauye-sauye a wannan fannin ba.A wani gefe, ya kawo gyara ko kuma kawo sauyi ga baki daya a wasu lamurran mutanen Makkah.Alal misali, ya rage tsawon geme.Daga karshe kuma akwai wasu al’adun mutanen Makkah, da ya yi watsi da su har illah mashallah..

A yau ma, wannan halin da Manzo ya nuna,kuma wanda a yau ake kira da “Kusancin da ya dogara kan zurfaffen nazari”,ra’ayi ne da ke da matukar muhimmanci ga Yammaci, Gabashi,Kudanci da kuma Arewacin duniya.Bugu da kari wannan tsarin ya yi daidai da alkiblolin “Wayewa”, na “Kan-ta-waye”, na “Duniya a tafin Hannu” da kuma duk wani sashen rayuwarmu.Ra’ayoyin “Mika Wuya” manyan kantangu ne tsakanin mu da karan kanmu.Ra’ayoyin “Yin Watsi” da komai a makance, na ingiza keyar matasa shiga kungiyoyin masu tsaurin ra’ayi ,kamar su DAESH.Shi yasa ka’idar “Duk abinda ba a haramta ba, halal ne” ta dokar Daular Usmaniyya ke da matukar muhimmanci.Wannan ra’ayin da ya yi daidai da ka’aidojin rayuwa na iya taimakawa haikan wajen kubuto wasun gungun mutanen da a yau suke kokarin magance matsalolin da ke nasaba da tunanin rashin nasara da suke fama da shi.

A yawancin lokuta Illahirin halayyar da ake  nunawa a  gwagwarmayar kawo gyara na Daular Usmaniyya,sun kasance a tsakiyar ra’ayoyin “Yin Watsi” da na “Sukar Lamiri”.Shi yasa, duk wasu lamurran da suka danganci wadannan sauye-sauyen basu shafi ra’ayoyin wannan zamanin kadai ba.Akwai wani tafarki da aka hau a wancan lokacin, wanda kawo yanzu a ke ci gaba da ganin sakamakonsa.A yau ma, yawancin soke-soken lamiri da muke shaidawa,sun samo asali ne daga sauye-sauyen ra'ayoyi ko kuma alkiblolin wancan zamanin.Saboda idan ba haka ba, babu ta yadda za a yi a dinka zuba na mujiya kan haiyayyafar ra’ayoyi da kuma  sauye-sauyen tunani bila-adadin da rayuwa ke gabatar mana a kulli yaumin, ba tare da mun yi wani abu ba.Wadannan sauye-sauye ne da ke matukar tasiri kan rayuwa daidaikun mutane, al’umomi,kamfanoni, da kuma jama’a,kana ke wahalda su matuka gaya.Ba zamu taba iya cewa, hadakan kasashen Turai ya taka wata rawar a zo a gani a wajen bullowar ra’ayin “Duniya a tafin hannu” ba.A nan, ba a ambaci wata mafita a lamarin cigaba ba a ilimance.Duk da yake, babu makawa, za a bunkasa wasu lamurran a matsayin mafita.Amma duk lokacin da kuma rungumi irin wannan cigaban,sai mu kasance cikin kadaici,kana mun ware kanmu daga wasu ababe da ke wakana a duniya.

Kamata ya yi mu juya wa ra’ayoyin “Mika Wuya” da na “Yin Watsi” a makance, baya, don hawa kan turbar “Kusancin da ya dogara kan zurafaffen nazari”.A gefe daya kuma,bai dace ba mun dinka fifita tunanin babu abinda zai taba gyaruwa,ko kuma ware kanmu daga lamurran da suka jibanci rayuwarmu ta yau da kullum.Islam ba wahala ba ce,sauki ne.Ba tsaurin ra’ayi ba ne,daidaici ne,addini ne na tsaka-tsakiya.

Daga karshe muna iya cewa, dukannin sassan duniya,wadanda a ciki har da Yammaci, bai kamata ba mun dinka rungumar tunanin rashin nasara a duk lokutan da muka ci karo da sabbin ababe,ra’ayoyi da kuma matsaloli,don waiwayar ababen da suka tabawa wakana a baya,kallan yanayin da muke cikinsa,don magance komai cikin ruwan sanyi da hikima.Musulmai mun arzuta tunani da kuma al’adunmu ta hanyar yin watsi da marar kyau da kuma aron nagari, a duk lokacin da muka yi cudanya da wasu al’adun da suka sha bamban da namu.Kamar yadda kwallon kankara ke kara girma a duk lokacin da ya gangara a kasa, haduwar mu da sauran al’umomin duniya, ba tsoron ta haifar mana ba,taska ta zamo ta arzkinmu.kamar yadda muke gani,warware bakin wannan zaren,ba abu ne da ke da matukar wahala kamar yadda ake tsammani.Kamar yadda Babban Fakihin daular Usmaniyya, Maulana Jalaluddin Rumi ya ce a littafinsa na “Pergel Metaforu”,kamata yayi a tashin farko mun san gaba da bayan al’adu, tarihi da kuma zamantakewarmu kafin mu bude hannayenmu zuwa sauran duniya,al’adu,al’umomi don bunkasa saninmu da kuma bude tunaninmu kan duniya da ababen da ke cikin ta.Wannan zai taimaka haikan wajen sauwake rayuwarmu da kuma tausasa zukatanmu kan ra’ayoyin da suka sha bamban da namu.

Ayar tambaya  a nan ita ce, shin ra’ayoyin da aka gina kan ginshimkai nagari su kadai na iya iya warware dukannin matsalolin duniya ? Shin akwai yiwuwar hakarmu ta ci ma ruwa ?

 Labarai masu alaka