Evangelism: Tirsasa Ubangiji busa kaho, tsunduma bil adama halin ha’ula’i

Sharhin farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami'ar Yıldırım Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

Evangelism: Tirsasa Ubangiji busa kaho, tsunduma bil adama halin ha’ula’i

Matsalolin Kasashen Duniya: 32

A wannan lokacin da muke ciki,  a fagen siyasar Turkiyya,sabili da mugayen ababen da kungiyar ta’adda ta FETÖ ta bari a baya,ana ci gaba da cece-kuce kan alakar da ke tsakanin shugabancin kasa da addini.A yawancin lokuta muna kyautata zaton cewa  mafiya lamurran da ke afkuwa a wasu kasashen, na da alaka da mu,shi yasa ranmu ke tsananin baci.Amma matakin da Amurka ta dauka kan Turkiyya game da batun Fasto Andrew Bruson, ya kara nuna wa duniya cewa, ba haka abin yake ba.

Kafin a fara tuhumar fasto Andrew Brunson bayan yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli,al’umar Turkiyya ba ta da wata masaniya game da aiyukan yada addinin Kiristanci da ya jima yana yi a kasarsu.Shawarar da Amurka ta yanke ta kakaba wa Turkiyya takunkumin kan fasto Brunson wanda aka kama da laifin tallafa wa haramtattun kungiyoyin PKK da FETÖ,ta sa mutane dasa aya kan dangantakar da ke tsakanin shugabanci da addini a Amurka.Ko da mun kalli lamarin ta fannin ‘yancin gudanar addini,amma tunanin kowa na ci gaba da cin karo da tilashin karkata kan mu’amalar da ke tsakanin gwamnatin Amurka da addini.Saboda babu wata fassarar da za a yi wa kalaman wancakali da yarjejeniyoyin kasa da kasa da hukumomin Amurka suka furta.

A hakikannin gaskiya, a kowace kasa, ingantacciyar mu’amala tsakanin addini da shugabanci, abu ne da bai kamata a ce ya tayar da hankali ba.Akasin haka, wannan lamari ne da ke da matukar kyau musamman ma a fannin  ‘yancin gudanar addini.Har ya zuwa wani makusancin zamani,duniya na ci gaba da yi wa Amurka, wacce Turawan yamma suka kafa, bayan sun guje wa datse-datsen kanu na azzaluman malaman Kirista masu tsauraran ra'ayoyi da nuna wariya, a matsayin kasar da ta fi kowace kare hakkin gudanar da addini ga kowa.

Kamar yadda samun kyaukyawar fahimta tsakanin shugabancin kasa da na addini ba abin kushewa ba ne, haka zalika tafiyar da aiyakun kasa kan tafirkin addini ma,ba zai taba zama abin Allah wadai ba.Duk addinin da ke kallon kabilu marasa rinjaye da idon basira,mai yin maraba da ra’ayin kowane dan kasa, ba zai taba haifar da cikas a fannin kare hakkoki da ‘yancin bil adama ba.Hasali ma,irin wannan lamarin na iya zama kalubale ga yunkurin kasashen duniya masu akidar mulkin mallaka.Misali mafi kyau na wannan lamarin, shi ne Daular Usmaniya,inda addini ya fi tasiri.

Abin da ya kamata a ce an yi tsayayya kansa, ba wai kallon alkibla daya da shugabanin kasa da na addinai suka yi  kan kare ‘yanci da kuma hakkokin bil adama.Abin yin tofin Allah tsine a kai shi ne,fakewa da addini da wasu kasashen ke yi don cim ma bururrukansu na mulkin mallaka.Akasin haka kuma, kamata ya yi addini ya hana fakewa da mulki don cim ma akidojin mulkin mallaka, ba tare da an kafa wata ka’aida,kallafa wata dabi’a da kuma kuntatawa ba.Za mu iya bada Isra’ila, kasar addini ko kuma addinin kasar Yahudu,wato sahyoniyawanci a matsayin babban misalin gurbacewar alaka tsakanin shugabanci da addini.Musulmai,Kirista da kuma Yahudawan da suka share shekaru aru-aru suna rayuwa tare a Falasdinu,sun kasa zama tare da kuma samun sukuni a karkashin mulkin Isra’ila.

Bari mu kara waiwayar Amurka,inda ake ci gaba da cewa,dan darikar Evangelism fasto  Brunson da kuma sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo,wanda a yanzu haka yake ci gaba da kai ruwa rana wajen ganin an kakaba wa Turkiyya takunkumi,’yan darika daya ne.’Yan wannan shiyyar kiristanci na da matukar tasiri a siyasar Amurka, kana sun mamaye yawancin madafan aikin kasar.Haka zalika, an tabbatar da cewa,akwai akalla ‘yan Evangelist milyan 90 a Amurka,wadanda a ciki har da tsaffin shugabannin kasar Amurka,Reagan da George W Bush junior.Shi yasa, komai na kara yin nuni da cewa, lamarin fasto Brunson ba batu ne ba da jibanci Turkiyya da Amurka.Abu ne da ya danganci Amurka da ‘yan darikar Evangelist da ke kasarta.

Shin ko mece ce darikar Evangelism ?

Abu na farko da ya kamata mu sani a nan shi ne, darikar Evangelism ta sha bamban da Shiyyar Kiristanci ta Ortodox da ta Katolika,saboda mazhaba ko kuma mu ce darika ce ta shiyyar Kiristancin Protestant.Wannan mazhabar ta fara bambanta da sauran shiyyoyin Kiristanci a karni na 19 miladiya.Ma’anar kalmar Evangelism ita ce “Karkata alkilba zuwa tsarkakken littafi”. Ba wai littafin Injila wanda tsarkakke ga mabiya addinin Kiristanci kawai ‘yan wannan mazbahar suka yi imani da shi ba, har da littafin “Tsohon alkawari”,wanda tsarkakke ne ga mabiya addinin Yahudu.A cewar ‘yan wannan darikar, a karshen duniya Kiristanci zai mulki duniya, inda daga bisani za a busa kaho.Amma kafin wannan lamarin ya akfu, za a kwashe lokaci mai tsawon gaske.Shi yasa suke kokarin gaggauta afkuwar wannan babban lamarin.Bambancin Evangelism da sauran darikun Kirista,shi ne,a cewar ‘yan wannan mazhabar, Yahudawa zababbu ne daga Allah,Falasdinu kuma hakkinsu ne,shi yasa kamata ya yi duk wani Kirista ya tallafa musu wajen kwato wannan kasar.

A cewar Dakta Özcan Güngör, bakon da muka yi a wannan makon a shirin Çeşmi Cihan na kafofin TRT da na TSR na Turkiyya,don yada mulkinta a duk fadin duniya,darikar Evangelism ta kafu kan ginshikai 7.A tashin karfo, kamata ya yi Yahudawa sun koma Falasdinu,wanda za mu iya cewa kusan sun cim ma wannan matsayin.A mataki na biyu, za a kafa Isra’ila wacce za ta kunshi wani bangare na kasar Turkiyya.A cewar wasu majiyoyi,nacin da Trump ya yi na maida Qudus,helkwatar Isra’ila, duk da hada karfi da karfe da kasashen duniya suka yi don kalubalantar sa da kuma maida shi saniyar ware a zauren Majalisar Dinkin Duniya,na da nasaba ne da tasirin da ‘yan Evangelism ke da shi a siyasar Amurka.Saboda a hakikannin gaskiya, cim ma wadannan manufofin ta hanyar dogaro da kyaukyawar aniya, abu ne mai matukar wuya.

Mataki na uku shi ne,yada sakon littafin Injila a duk fadin duniya.Akwai yiwuwar sama da shekaru 10 da fasto Brunson ya share a Turkiyya na da alaka da wannan manufar.To sai dai, ba a Turkiyya kadai ba ‘yan Evangelism ke yada akidojin mazhabarsu.A yanzu haka ‘yan wannan darikar na ci gaba da yunkurin kiristantar da al’umomin kasashen Musulmai,musamman ma na nahiyar Afirka,inda tuni milyoyi mutane suka rungumi akidarsu.

Mataki na hudu shi ne,samar da shekaru bakwai na musiba mai radadi a duk fadin duniya.

Mataki na biyar shi ne,dawowar Annabi Isa (A.S) karo na biyu doron duniya.

Mataki na shida shi ne, ‘yan darikar za su jagoranci wani kazamin yakin duniya da za a tafka  a nan gaba,wai shi “Yakin Armegedon” tsakanin masu imani da marasa shi.Da yake a karshen wannan yakin ‘yan Evangelism ne za su yi nasara,dole ne a yi kadaran-kadahan don fadada kasar Isra’ila.

Mataki na bakwai kuma shi ne,Kiristanci zai mulki duniya,kana a yi tashin kiyama.

Kamar yadda muka yi la’akari,daga matakin farko har ya zuwa na shida,dukanninsu na da nasaba ne kacokal da akidojin sahyoniyawanci.Shi yasa ma, ake kiran ‘yan Evangelism da suna “Sahyoniyawan Kiristoci”.

A karni na 19 miladiya ne aka fara gabatar da Evangelism a matsayin daya daga cikin addinan da aka kafa kan akidojin kadaita Allah, kamar Yahudanci,Musulunci da kuma Kiristanci.Da yawa daga cikin sahyoniyawan Yahudawa,wadanda a ciki har da Teodor Herlz sun gurbata akidojin Yahudanci kafin sun cim ma burinsu na kafa Isra’ila.Shi yasa a yau, akwai Yahudawa da dama ke ci gaba da yin watsi da akidar sahyoniyawanci.A wani zamani da ya shude, Turkiyya da wasu kaashen Musulmai sun yi kokari samar da wata sabuwar kalar Musulunci,wacce ke iya zama kalau da akidar sahyoniyawanci.Batutuwa kamar su “Musayar Yawu Tsakanin Addinai Mabambanta” na daga cikin ababe marasa tushe a karantarwar Islama, ta hanyar yin gurbatattun fasarce-farsarce da kuma yada mugayen halayya.Kamar ‘yan Evangelism,wadannan mutanen ma, sun yi imani da cewa,Falasdinu gado ne na Yahudawa halak malak.

Sabili da rikice-rikicen addinai mabambanta da na tarihi,abu ne da ya kamata a ce yana da matukar wuya a samu bullowar wata sabuwar shiyyar Kiristanci mai yin na’am sahyoniyawanci.Yiwuwar cewa wannan yunkuri ne na sahyoniyawan Yahudawa,abu ne da ke ci gaba da karfafa a zukatan mutanen duniya.Akwai Kirista da dama ke ci gaba da Allah wadai da akidar Evangelism (Kiristancin sahyoniyawanci).Kowa ya shaida halin da Papa Roman darikar Katolika ya nuna na kin maraba da matakin Amurka na maida Qudus, helkwatar Isra’ila.Haka zalika, ‘yan Ortodox ma, na sukar darikar Evangelism,inda a wani sa’ilin suke goya wa Musulmai baya don yin tofin Allah tsine kan azzalumar kasar Isra’ila.

Tirsasa ubangiji busa kaho ba hakki ne na dan adam.Amma tsunduma bani adam a halin kaka-ni-kayi,lamari ne da babu tantama a kansa a halin da muke ciki.Kamata ya yi a sake zage damtse wajen hana wa darikar Evangelism cim ma mummunar akidarta ta jefa duniya cikin halin ukuba da ha’ula’i.Amma wannan hakar ba za ta taba ci ma ruwa ba, fa ce sai dukannin Musulmai,Yahudawa, da kuma Kiristocin fadin duniya ,wadanda kawo yanzu ba a wanke kwakwalensu ba, sun zama tsintsiya madaurinki daya.

 Labarai masu alaka