Jiragen kunar bakin wake marasa matuki na Turkiyya

Yayin gwagwarmayarta ta kauda ta’adda, Turkiyya ta nuna bukatarta ta sayen jiragen kunar bakin wake marasa matuka daga Amukra,fakat Amurkawa sun yi kunnen uwar shegu.

Jiragen kunar bakin wake marasa matuki na Turkiyya

A yau, a karo na farko, Turkiyya ta kera jiragenta na kunar bakin wake marasa matuka ALPARU da KARGU, da kuma jirgi marar matuki mai leken asiri TOGAN.

Muna gabatar muku da sharhin Tarkan Zengin, shugaban horo na kungiyar kwadago ta masana’antar kera makaman yaki ta Turkiyya.

Turkiyya na ci gaba da jan hankalin duniya, sakamakon makaman yakin da ta kera a ‘yan shekarun nan.A kowane fannin rayuwa, ana amfani da jirage marasa matuka, wadanda na’urori ne da ake aiki da su a da a fagen fina-finai, don daukar hotuna daga sararin samaniya.A yau, Turkiyya ta fara kera jirage marasa matuka, wadanda ke da matukar amfani a fagen yaki da ta’addanci.Kasar ta so Amurkawa su siyar ma ta da jiragen kunar bakin wake marasa matuka,amma suka ki.Halin da Amurka ta nuna na kin siyar wa Turkiyya,babban abokiyar ittifakinta a Gabas ta Tsakiya,da wadannan makaman masu tasiri haikan wajen kauda ta’addanci, abu ne mai ban mamaki kwarai da gaske.Ko da yake tuni Turkiyya, ta yi amfani da wannan damar don kera wadannan kayayyakin yakin da karan kanta, da kuma aiki da su.Har ta kai, wasu kasashen ketare suka fara odar makaman daga gare ta.Wannan na daya daga cikin manya-manyan nasarorin da Turkiyya ta samu.Soboda ta kasance a sahun kasashe 3 na duniya,wadanda ke kera jiragen kunar bakin wake marasa matuka.

Turkiyya ta ci cim ma wani muhimmin matsayi a fannin fasahar kera jirage marasa matuka.Tuni ta wuce matakin kera wadannan na’urorin wadanda ake yi wa taken “Sabbin sojojin Turkiyya a samaniya”, inda a yau jami’an tsaronta ne ke aiki da su.

Bari mu gabatar muku  da uku daga cikin jiragen marasa matuka da kwararru a masana’antar tsaron Turkiyya suka kera. Jirgi marar matuki mai saraffa kansa da kafaffun fika-fikai,ALPAGU,jirgi marar matuki mai saraffa kansa wanda fika-fikansa ke juyawa, ,KARGU da kuma Jirgi marar matuki mai saraffa kansa da leken asiri,TOGAN.Ma’aikatar cinikaiya da bunkasa fasahohin makaman yaki,masana’anta ce da  sojoji tare da tallafin kwamitin zartarwa na masana’antar tsaron kasar Turkiyya suka kafa, da zummar kawo tallafi a fannonin da suka hada da habbaka fasahohin kera makaman yaki,tsara aiyukan tsaro da kuma safarar fasaha daga ketare zuwa Turkiyya.

An fara mika wa runduna ta musamman da ta ruwa ta Turkiyya, jiragen kunar bakin wake marasa matuka wadanda kasarsu ta kera, a karo farko a  watan Nuwamaban shekarar 2017.An yi amfani da KARGU a hare-haren tabbatar da tsaro na Reshen Zaitun.A fagen wannan gwagwarmayar jirgi ya farauci wasu ‘yan PKK 5 da suka ari na kare,inda ya aika su barzahu ta hanyar fashewa a lokacin ya cim musu.A dalilin wannan jirgin ne jami’an tsaron Turkiyya suka gano mabuwar ‘yan ta’addar PKK daga tazarar kilomita 5.Bayan Afrin, a yanzu haka na’urar ta zama abin tsoro ga ‘yan hamratattuun kungiyoyin ta’addar da ake ci gaba da fatattaka a Kandil.

ALPAGU (Jirgi marar matuki mai saraffa kansa da kafaffun fika-fikai)

Jiragen marasa matuka na Turkiyya na a jerin kayayyakin yaki mafiya inganci da Alfano a fagen gwagwarmaya da ta’addanci.Mana’ar ALPAGU it ace, “Gwarzo daya tak mai far wa makiya”.Saboda soja daya tilo kan iya tada jirgin,mai fasalin gano mabuyar makiya tare da halaka su kai tsaye.

A cewar ma’ikatar tsaron kasar Turkiyya wacce it ace ta kera ALPAGU,jirgin na da fasololi kamar haka:Bincike da kuma gano duk inda hadurra suke don kauda su.Tanadar na’urorin daukar hoton da ke gani har hanji da kuma wallafa su a kai tsaye.Ana iya amfani da ALPAGU ta ingantacciyar hanya kan hadurran da ke kafe ko kuma motsi.

KARGU (jirgi marar matuki mai saraffa kansa wanda fika-fikansa ke juyawa)

Ma’anar KARGU, ita ce, “ Hasumiyar leken asiri ta kan tsauni” ko kuma “Shaho”.Haka zalika ana kiran sa da “jirgi marar matuki mai saraffa kansa wanda fika-fikansa ke juyawa”.A cewar ma’aikatar tsaron kasar Turkiyya wacce it ace ta kera wannan na’urar,jirgin na da fasololi kamar haka: Tana sarrafa kanta ko kuma ana  iya sarrafa ta hanyar amfani da masarrafin tafi da hannunka.Tana da fasahar " luguden wuta da ta juya fika-fikai,VİHA" da kuma tsarin " Tabbatar da tsaro a doron kasa".KARGU na iya kaddamar da farmakai dare da rana.Bugu da kari, bayan fasalin kai harin kunar bakin wake, ta tanadi tsare-tsaren kai hari iri daban-daban da kuma fasahar tsara tazarar kai farmaki  da ta harbi da karan kanta.

TOGAN (Jirgi marar matuki mai saraffa kansa da leken asiri)

Mana’anar TOGAN, it ace “Tsunstun da ka iya amfani da kaifin ganinsa don gano hadari a duk inda yake, da kuma amfani da fika-fikansa masu karfi don zana da’irori a sararin samaniya”. A cewar ma’ikatar tsaron kasar Turkiyya wacce it ace ta kera na’urar,jirgin na da fasololi kamar haka:Gudanar da aiyukan leken aisi da gano hadurran yau da kulllum.Tanadar tsarin shawo kan matsalar tsara aiyuka mai zaman kansa,hazaka da kuma cikakkiyar damar sarrafa kansa, wacce ke ci gaba da bai wa duniya mamaki, na daga cikin fasalolinsa mafiya jan hankali.

Wadannan jiragen marasa matuka basu bai wa ‘yan ta’adda damar aron na kare ba.Saboda sun tanadi fasalolin halaka su duk a inda suke,kuma komai kankantar mabuyarsu.Ana iya shirya ALPAGU da KARGU tare da harba su samaniya cikin kankanin lokaci,wato kasa dakika daya tak.Jiragen wadanda ke gudun kilomita 120 zuwa 140 a sa'a, na iya cimma matsayinsu kai tsaye.Haka zalika sun tanadi fasalolin daukar harsasai da na halaka duk wani abu da ke a yanki mai girman murabbin mita 20.Wadannan na’urorin yaki da Turkiyya ta kera na ci gaba da jefa tsoro a zukatan ‘yan ta’adda.Labarai masu alaka