Ra’ayoyi uku kan Yammacin Duniya

Sharhin Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami'ar Yıldırım Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

KÜRESEL PERSPEKTİF 31 (1).jpg
KÜRESEL PERSPEKTİF 31 (2).jpg

Matsalolin Kasashen Duniya: 31

Idan muka waiwayi tarihin shekaru 200 da suka gabata,sai mu gane cewa, daya daga cikin lamurran da suka dinka kai kawo a kwakwalen manazarta tun a zamanin daular Usmaniyya zuwa kafuwar Jamhuriyyar Turkiyya shi ne, kowace irin alaka ya kamata mu kulla da Yamma ?Ainahin musabbabin wannnan musayar yawun da aka kwashe shekaru aru-aru ana yi kan batutuwa daban-daban,wadanda suka hada da bukatar kawo sauyi, wayewar yammacin duniya,Tarayyar Turai da kuma sabuwar akidar dunkule duniya a tafin hannu,shi ne kafa ginshikin lamarin da ya fi ci wa kowa tuwo a kwarya,wato alakarmu da yammacin duniya.

An rawaito cewa mazanartan karshe na daular Usmaniyya sun gabatar ra’ayoyi uku kan Yammacin duniya. “Mika Wuya”, shi ne ra’ayi na farko,wanda marubuci kana shugaban mujallar “Ijtihad”,Abdullah Jevdet ya gabatar. A cewarsa,akwai wayewa daya tak a duniya,kuma it ace ta Turai.Shi yasa kamata ya yi a mika wuya ga wannan wayewar kungurungu,in ba haka ba,mu zama tatsuniya ga na baya.

Ra’ayi na biyus hi ne, “Yin Watsi”.Wannan ra’ayi na da’awar yin wancakali da duk wani abu da ke alaka da wayewar Turai,saboda yammacin duniya, tushe ne na duk wata fitina da musiba.

Ra’ayi na uku kuma shi ne,“Hikima” ko kuma “Aminci”.Wannan matsayin wanda bai yi inkarin akidar jari hujja ta yammacin duniya ba,ya kasance na tsaka-tsakiya,wato tsakanin ra’ayoyin“Mika Wuya” da na “Yin watsi”,don kallon wayewar Yamma da idon basira.Saboda kar kyamar da muke yi wa Turai,ta makanta mu har ta hana mu ganin fannoninta nagari da kuma namu mugayen halayen.Ana iya la’akari da wannan ra’ayin a aikace a halin da wazirin daular Usmaniyya Said Halim Pasha ya nuna lokacin yakin duniya na farko.A cewarsa, duk da ire-iren ababen da suka afku, kamata yayi yammaci da kuma gabashin duniya su mika wa juna hannu don kallon alkibla daya.Haka zalika ya ce, ba Yamma kadai ke da laifi ba a wutar gabar da ke ci tsakanin ta da Gabas.

Saboda a ganinsa, idan bera na sata,to daddawa ma na da wari.A littafinsa na “Taassub”, Pasha ya ce ainaihin manufar tunaninsa, ba wai kara rura wutar kiyayya da ke tsakanin al’umomin wadanda duniyoyin 2 ba ce.Bukatarsa ita ce, kauda duk wani kalubale da kuma gurbataccen tunanin da ke hana ruwa gudu a kokarin gabatar wa gabashi da Yammacin duniya tilashin da suke shi na rayuwa tare,kulla kyaukyawar alaka da fahimtar junansu.

Gurbatattun ra’ayoyi da sakamakon da suka haifar

Wannan musayar yawu ce da kawo yanzu ake ci gaba da yi.Watakil a yau ta fi zama zazzafa fiye da zamaninnikan baya.A yanzu, zai yi wuya a gane iyakokin Gabas,Yamma, Kudu da kuma Arewacin duniya,saboda yadda akidar “Globalization”,wato “Dunkulewar Duniya a tafin hannu” ta samu gindin zama.Dukannin yankunan duniya sun kusanta da juna matuka gaya.A yau, zai yi wuya wata kasa ta ware kanta daga sauran sassan duniya don kare al’adu da kuma wayewarta.

A yau akwai milyoyin masu neman mafaka da kuma Musulmai da ke rayuwa a Yammacin Duniya.Saboda haka za ku iya yin watsi da tunanin da masu rayuwa a ketaren yammacin duniya ke da shi kan Turai don ci gaba da musayar ra’ayi kan wadanda ke rayuwa a cikinta.Don wannan matsalar ta fi tasiri kan su,musamman ma gurbatattun ra’ayoyi,wadanda ka iya haifar da mummunan sakamako.A gefe daya kuma,matsayin wadanda ke rayuwa a ketaren Turai ma,na da nasaba da ra’ayoyi uku da muka ambata a baya.

A yau ma,  kamar a daular Usmaniyya,kawunan masu neman mafaka da na Musulman Turai sun rabu kan ra’ayoyi biyu, na “Mika Wuya” da na “Yin Watsi”.Rashin galaba da matsalolin rayuwa sun sa mutane rungumar ra’ayin mika wuya ga wayewar Turai ko kuma yin watsi da ita.Mutane sun samun  ‘yanci a kasashen kamar su Ostireliya,Amurka da kuma Kanada, inda al’umomi masu mabambantan al’adu ke rayuwa salim-alim.A wadannan kasashen masu neman mafaka da Musulmai, ba su da wani mugun kallo kan al’umar kasar da suke rayuwa a cikinta,yayin da na kasashen Turai kuma, kanunsu suka rabu haikan kan ra’ayoyin “Mika Wuya” da na “Yin Watsi”, sabili da wulakanci, gallazawa da kuma kokarin kauda al’adu,tarihi da kuma addinansu da ake ci gaba da yi, babu kakkautawa.

 “Yin Watsi”,ra’ayi ne na wadanda  aka ki amincewa da al’adunsu a kasashen Turai, wanda hakan yasa suka yi watsi da duk wani abu da ke alaka da kasashen da suke rayuwa a cikinsu.İllahirn wadanda suka rungumi wannan tsatssaucin ra’ayin, na datse dangatakar da ke tsakanin su da al’umomin da ke rayuwa a wadannan kasashen.Bugu da kari, bayan wani lokaci mai tsawo, wadannan mutanen ba za su karu ko kuma amfanar kasashen da suka karbi bakwancin su da komai ba.Shi yasa idan aka ware Afganistan, Iraki da kuma Libiya,wadanda kasashen Turai suka mamaye,kungiyoyin ta’adda kamar su DAESH sun fi barna a Yammacin Duniya.Saboda wadannan haramtattun kungiyoyin sun zama tamkar wata hanyar billewa, ga mutanen da Turai ta maida saniyar ware,duk da cewa yawancin su na jin harsunan Turai da dama,wadanda suka hada da Ingilishi,Faransanci,da kuma Jamusanci.Inda an ba su kyaukyawan matsayi, da wadannan matasan sun zama ababen alfahari ga Turai da kuma kasashensu na ainahi.Banda gushewa daga doron duniya,babu wata makoma ga irin wadannan mutanen da kuma kasashen da suka karbi bakwancin su.Don wannan dalilin ne,wasu kungiyoyin leken asiri na Turai da kungiyoyin da ke kyamar cudanyar al’umomi ke tallafa wa ‘yan akidar “Yin Watsi”,inda har suke kokarin yada tunaninsu a kasashen Musulmai.

Wani matsayi na daban da masu neman mafakar da ke rayuwa a Turai ke iya runguma shi ne, “Mika Wuya”.A irin wannan matsayin,gwamnatocin da kasashen da suke rayuwa a cikinsu,sun rufe dukannin kofofin kubuta da kuma samun ‘yanci.Shi yasa baki ke yin watsi da al’adu, tarihi,addini da duk wani abu da shafi kasashensu na ainahi don mika wuya ga wayewar kasashen da suka bakwancinsu.İre-iren wadannan mutanen ba su da wata fa’ida ga kasashen da suke ciki a yanzu, saboda sun rasa amincinsu ga baki daya.Shi yasa a duk tsawon rayuwarsu,suke kokarin fa’idantar kasashen da suke rayuwa a cikinsu.Saboda a tunaninsu, wannan shi ne abinda ake bukatar su yi.Kazalika suna tayar da hankali kan ainahin makomarsu a kasashen da suka karbi bakwancinsu,abinda yasa a kulli yaumin suke kaskantar da kansu, al’adu da kuma kasashensu na ainahi.Wannan lamarin ya samo asali ne daga rashin aminci ko bukatar gabatar da sabon abu a ko yaushe.Akwai yiwuwar wannan ne dalilin makauniyar kyamar da wasu daga cikin masu neman mafakar da suka yi watsi wa kasashensu na ainahi,bayan sun rungumar wayewar Turai daga kai har kwakwarta.İdan har shugabannin kasashensu ainahi na wadannan matafiyan da kuma sauran masu neman mafakar da ke ci gaba da alfahari da al’adunsu,  suka fara yi wa wannan lamarin mummunar fahimta, to shakka babu alakar da ke tsakanin kasashen ainahi da kuma wadanda ke karbar bakwacin za ta yi matukar gurbacewa.

Shin mece ce fa’idar ra’ayin da aka gina kan Aminci da Hikima ? Wannan ita ce ayar tambayar da zamu yi kokarin bada amsarta a nan gaba.Labarai masu alaka