Shari'ar NSU da karuwar nuna wariya a Turai- Nuna Kyamar Musulunci

Duk da an kawo karshen shari'ar da ake yi da kungiyar ta'addar NSU masu ra'ayin nazi da aka kwashe shekaru biyar ana saurare a Jamus, kungiyar bata tuba daga aikata aiyukan da ake zarginta da yi ba.

Shari'ar NSU da karuwar nuna wariya a Turai- Nuna Kyamar Musulunci

Kungiyar ta'addar NSU masu tsattsaurar ra'ayi na ci gaba da aiyukan nuna ƙyamar baƙi, nuna wariyar launin fata da kuma kyamar lslama.

An dai kawo karshen shari'ar da ake yi da kungiyar ta’addar Nationalist Socialist Underground (NSU) da aka kama da laifuffukan kashe mutane goma da takwas daga cikin su Turkawa ne, fashi da makami a bankuna da kuma kai hare-haren bama-bamai. Bayan babban kotun Munich ta kwashe shekaru biyar ta na sauraren ƙara, ta yankewa jagaban aiyukan ɓarnan da kungiyar ke aiyanarwa Beate Zschaepe hukumcin ɗaurin rai-da-rai ta kuma tasa ƙyeyar mataimakansa huɗu gidan waƙafi na tsawon shekaru daban-daban ko wannensu.

Kamar dai ko wacce sati akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da malam Yazar Can ACUN daga cibiyar nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA.

Alƙalai da jami'an tsaron ƙasar Jamus sun bayyana cewar Kungiyar NSU mutane uku suka ƙirƙirota. Baya ga Beate Zschaepe akwai mambobin da suka haɗa da Uwe Bohnhard da Uwe Mundlos. Su biyun an bayyana cewar an gano su amace bayan fashin da suka aiyanar a wani banki a ranar 4 ga watan Nuwambar 2011. An dai yi hasashen sun kashe kansu ne sabili da wasu dalilai. Bugu da kari, abubuwan da suka bayyana, bayan jagoran kungiyar da magoya bayansa sun buɗewa wani gida wuta da daga bisani ƴan sanda suka kamesu da kuma yadda hukumar tsaron ƙasar ta ƙi fita bayansu, a inda kuma ta lalata kundi 130 da keda alaƙa dasu da kuma yadda lauyoyin ƙasar basu taɓa amincewa da mutane uku ne suka kirkiri kungiyar ba na nuni da akwai lauje cikin naɗi game da harkokin kungiyar.

Duk da an kai ƙarshen shari'ar da ake yi da kungiyar wanda aka yankewa mambobin hukunci, har yanzu hukumar tsaron ƙasa bata fitar da wata takamaiman amsa akan munanar harkokin kungiyar ba.

Jami'an tsaron Jamus sunƙi amincewa da cewar aiyukan kashe-kashe da ƙungiyar ta'addar NSU ke yi suna da alaƙa da nuna wariyar launin fata da ƙabilanci. Haka kuma yadda kafafen yaɗa labaran Jamus basu kalli aiyukan ƙungiyar a matsayin laifi ba, da kuma yadda labaran da suke yaɗawa ke ƙin danganta ta’asar ƙungiyar da nuna wariyar launin fata da ƙabilanci sun sanya kungiyar samun damar ci gaba da aiyukan ta'addancinta; lnda har ta aiyanar da kissar mutane goma.

Daga cikin lamurkan dake nuna ana ci gaba da nuna wariyar launin fata da ƙabilanci a Jamus duk da ko an hukuntar da mambobin kungiyar ta'addar NSU sune ƙara ɗaukakar da jam'iyyar AfD mai tsattsaurar ra'ayi ta samu inda ta kasance jam'iyya mai daraja ta biyu a ƙasar. Hakan dai na nuni da cewa kyamar lslama da nuna wariyar launin fata sun sami gurin zama a ƙasar Jamus, ta'asar nuna wariyar launin fata, ƙabilanci da ƙyamar baƙi da aka jima ana fama da su a Jamus na shirin ƙara ɗaukar sabbin salo ganin yadda jam'iyyar AfD mai tsattsaurar ra'ayi ke ƙara ƙarfi a ƙasar.

Haka kuma, baya ga ƙarfin da jam'iyyar AfD mai tsattsaurar ra'ayi ta ƙara samu, jam'iyyar dake mulkin ƙasar ta Christian Socialist ma, na aiyanar da aiyukar ƙyamar baƙi da Islama kamar yadda AfD ke aiyanarwa. Tun bayan yaƙin duniya na biyu ba'a taɓa samun yaɗuwar nuna wariyar launin fata, ƙabilanci da ƙyamar lslama a ƙasar Jamus ba irin na halin da ake ciki yanzu.

Ɗaya daga cikin alƙaluman dake nuna ci gaban mai ginar rijiya da Jamus ta samu kanta ciki dangane da zamantakewa shi ne- yadda ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar ta kasance a halin yanzu. A shekarar 2014, a lokacin da ta ɗauki kofin duniya, kungiyar kwallon kafar ƙasar ta rungumi kowa, tana da haɗin kai, inda a wannan lokacin ƴan wasan da suka yi hijira zuwa ƙasar kamar su Mesud Özil, İlkay Gündoğan, Sami Khedira, Lukas Podolski da Jerome Boateng suka taka rawar gani a fagen nasarar da kungiyar ta samu. A halin yanzu nuna wariyar launin fata da ƙabilanci ya yi katutu a cikin kungiyar kwallon kafar Jamus, da farko dai, kalaman shugaban jam'iyyar AfD mai tsattsaurar ra'ayi Alexander Gauland da ya fito ƙarara yana nuna ƙyama ga ɗan wasa Boateng. Haka kuma, daukar hotunan da ƴan wasa Mesud Özil da llkay Gündoğan suka yi da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a Birtaniya ya gamu da ƙalubalanta daga masu tsattsaurar ra'ayi a Jamus, inda har ma ta’allaƙa shi a matsayin dalilin da yasa aka fitar da ƙasar Jamus tun tashin farko a wasan cin kofin duniya da aka gudanar a Rasha bana.Labarai masu alaka