A wannen matsayi za a iya ajje Yammacin Duniya?

Zamu gabatar muku da sharhin farfesa Kudret Bulbul Shugaban tsangayar nazarin Siyasa a Jami'ar Yıldırım Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

A wannen matsayi za a iya ajje Yammacin Duniya?

Matsalolin Kasashen Duniya: 30

A tsawon karnoki 2 da suka shude, banda Turai, kusan illahiri, ko ma mu ce, ga baki dayan al'umomin ketaren Yammacin duniya, na ci gaba da rikidewa don komawa Turawa.Wannan lamarin ya samo asali ne daga matsin lamban da Yammacin duniya ke ci gaba da yi wajen tirsasa wa duniya rungumar wayewarta.Dukannin al'umomin da suka fadi a mujadalarsu ta yin tawaye da tunanin Turai, na yanke shawarar kallon alkiblar Yammacin duniya a matsayin matakin kubuta na wucin gadi.Ko shakka babu, musabbabin faduwar kasashen a wannan jarrabawar, ba wai lamurran da ke wakana a Turai kawai ba ne.Watakil suna daga cikin muhimman dalilai,rashin seta tafiyar tarihi,al'adu da wayewar wadannan kasashen duba da rawar zamaninmu na yau.Haka zalika, kasashen sun kasa tabuka komai wajen daukar matakan da suka dace don kalubalantar duk wasu barazanonin da suka gitta a gabansu.Abu mafi a'ala shi ne,su dinka amfani da 'yancinsu wajen hangen nesa da kuma dauka matakan riga-kafi,idan har ba san son su zama tatsuniya ga na baya.

Babu makawa, wadannan al'umomin za su ci gaba da gwagwarmaya don ganin sun ci gaba da kasancewa a doron duniya.Amma rayuwa za ta ci gaba kamar a kulli yaumin.Ba a iya cewa, sai kasashen da ke ketaren Turai, "Sun sabunta kansu kafin su kulla alaka da Yamma".A gefe daya, yayin da suke ci gaba da wannan gwagwarmayar, a daya bangaren kuma,sun kasance masu karfafa dangantakar da ke tatsakanin gabas, yamma, kudu da arewa.Saboda rayuwa ba za ta taba tsayawa ba.A daidai wannan lokacin, za a iya dasa aya tambaya kamar haka: Shin ko yaya wadannan kasashen za su kulla ingantacciyar hulda da Turai ba tare sun juya wa komai nasu baya ba ? Ba za a taba kwatanta wayewar Islama da sauran wayewa marasa tushe da ginshikai nagari,wadanda suka kunno a shekaran jiyan tarihin bil adama ba.A tsawon karnoni da dama,wayewar Islama ta zama tamkar inuwar bishiya daya wacce a karkashinta al'umomin daga illahirin sassan duniya suka rayu cikin kwanciyar hankali da karrama juna, duk da cewa al'adunsu mabambanta ne.Shi yasa,ta tanadi ingantattun ginshikai da kuma kyaukyawar akibla mai haskaka hanyar al'umominta komai duhu.Wannan akiblar babbar mafita ce gare ta, musamman ma wajen magance matsalolin da ta ke fama da su a yau.Saboda a matsayinta na babban addini, Musulunci bai yadu ba a lokaci daya.Ya samu gindin zama ta hanyar warware baken zaren dukannin matsalolin rayuwa da suka dinka cin karo da shi a tsawon shekaru aru-aru.

Shin a daidai lokacin da kasashen da ke ketaren Turai ke ci gaba da fadi-tashin samar da sabbin matakan raya wayewarsu, ko cikin wane irin yunkuri ne yammacin Duniya za ta tsinci kanta ? Amsar wannan tambayar na da matukar muhimmanci ko a jiya, amma a yau ta zarce hakan.A tsawon karnoni 2 da suka gabata, tasirin da Turai ke da shi kan sauran kasashen duniya, na ci gaba da daduwa babu kakkautawa.Bugu da kari, a yau akwai milyoyin jama'a na kasashen wajen Turai, wadanda ke rayuwa a yammacin duniya.A kasashen da suke, alakar da wadannan jama'ar za su kulla da al'umomin Yamma na da matukar muhimmanci.Wutar kyamar Yamma na ci gaba da ruruwa a zukatansu, sakamakon yadda Turai ke ci gaba da kokairn salwantar da wayewarsu a kasashensu  na ainahi da kuma durkusar da su gaban tutar mulkin mallaka.Abu ne mai saukin gaske, gane dalilin kyamar da wadannan mutanen ke yi wa Turai, musamman ma wadanda aka yi wa mulkin mallaka.Amma a wani bangaren,wannan kyamar na tashi daga kan Turawa don shafar dukannin sassa na rayuwa.Alal misali za a iya samun kungiyoyin masu kyamar Turawa,masu adawa da tafiyar zamani,da 'yan jari hujja,da dunkulewar duniya tamkar kasa daya tilo,da daidai sauran su. Kyama, wata aba ce wacce a wani sa'ilin mutane ke iya fadada ta fiye da kima.Daga cigaban fasaha da kimiyya na gudun wuce sa'a da muke da shi a yau, ya zuwa dunkulewar duniya a tafin hannu,Turai,Sahyoniyanci, da ma dukannin fannoni na rayuwa, da dalili ko babu shi, kusan babu wani abu da wannan kyamar ba ta shafa ba.

Ko shakka babu akwai ababe da dama wadanda ke cusa wa duniya yin tsayayya gaTurai da wayewarta.Abu marar dacewa a nan shi ne, nuna makauniyar kyama marar tushe da makama, ba wai yin allah wadai cikin aminci da sanin-yakamata ba,Watakil,kyamar komai da kuma kowa babu gyara babu dalili, saboda  tsintar kai cikin halin kaka-ni-kayi da na kaskanci ko don bukatar mayar da matani,ya zama tamkar yayyafin da ya fito daga sararin samaniya don sanyaya zukatansu.Musamman ma matasa,wadanda kansewa cikin tumutsutsun jama'a ke iya kara rura wutar da ke ci a zukantansu.Kyama na iya rugurguza ababe da dama.Babu abin da za iya ganiwa kan ta.Saboda kiran mutum da abin ya ke kyama ko kuma ya ki,tamkar maida shi saniyar ware ne.Gabatar da kanka a matsayin mai kyama,tamkar mika wuya ne ga abinda ka ki.

A gefe daya kuma,shin  bayan tashe-tashen hankula marasa adadi, kazamar cacar-baki,mummunar dagulewar lamurra, kara yankewa daga rayuwa, duniya da kuma gaskiya, wacce irin riba ce kyamar da aka gina kan fito-na-fito, ke da ita ? Dukufa kan irin kyamar kawai,na nesanta mutum ne daga yi wa kai hisabi, neman mafita, yin watsi da hadakai, da kuma kara tsunduma shi cikin halin ukuba da ha'ula'i.A yawancin lokuta irim wannan kyamar na yi tsamari matuka gaya sabili da aika-aikan wadanda suka rungume ta.A yau,gurbatacciyar akalar da ke tsakanin kungiyoyi masu tsaurin ra'ayi da hukumomin leken asiri na kasashen Yamma, ta samo asali ne daga irin dangantakar da ke tsakanin mayakan Kirista na Salibiyyawa da makasan Hashashin na zamanunnukan baya.Abinda muka fi matukar bukata a yau shi ne,nesanta kanmu daga kyama da kuma rashin nasarar da ke kara zurfafa bakin ciki da kuma ukubarmu.Mu zama basu warware matsalolinsu cikin yarda da aminci, ba wai masu yin watsi da komai ido rufe ba.Shi yasa, mu guje wa zumudin kyama,wasi-wasin kalamai,mugun dadin baki,faduwa hannun ma'ilmanta masu yawan magana, don kulla alaka da kowane sashe cikin karamci da aminci.

Idan muka dubi matsalar ta wata tsigar, ba "kalubalantar Yamma" ba, "Yaya zamu Kusanci Yamma" ita ce ayar tambayar da ya kamata a dasa. Saboda furta jumlar "Kalubalantar Yamma" na yin nuni da girman matsalar da ke akwai, tun tashin farko.Dukannnin wani aiki da muka gudanar kan kyama, zai nesanta mu daga ainahin alkiblarmu don tirsasa mu mika wuya ga abinda muke kyama.Wannan irin kyamar na gabatar da Yamma a matsayin cibiyar duniya.Alhalin ko, Turai ce ya kamata a ce ta kalli addini, al'adu da kuma wayewar kasashen da ke ketaren ta, don ta dauke su a matsayin cibiyoyin duniya.Dangane da abinda ya shafe mu kuma, muna zana iyakokin tarihi da kuma al'adunmu duba da Musulunci da wayewarta.

Ayar tambaya da a yanzu zamu dasa ita ce, shin akwai bukatar mu kusanci Yammacin duniya duba da sharuddan da muke su a yau ? Wannan musayar yawun ba aba ce ba da aka fara tattaunawa a kan ta a yau kawai ba.An share shekaru dari biyu ana kace-nacen shawo kanta.Za mu ci gaba da yin tsokaci kan wannan batun duba da ire-iren ababen da muka shaida a baya.Labarai masu alaka