Aiyukan Kasar Turkiyya a fagen tsaro (2)

Zamu gabatar sharhin shugaban horo na kungiyar kwadago ta masana’antar kera makaman yaki ta Turkiyya, Tarkan Zengin.

Aiyukan Kasar Turkiyya a fagen tsaro (2)

Kera jigin ruwa mai tafiya karkashin teku da na yaki mai sintiri,Milgem,na daya  daga cikin manya-manyan aiyukan kera kayayyakin yaki wadanda Turkiyya ta gudanar bisa  umarnin masana'antar kera jiragen ruwa ta birnin Santambul.Ya zuwa yanzu masana’antar ta kera jiragen ruwa 4 wadanda Turkiyya ke bukata, inda kasar Pakistan kuma ta yi odar wasu 4 daga gare ta.
Jigin ruwa mai tafiya karkashin teku da na yaki mai sintiri,Milgem,kayayyakin yaki ne da sojojin Turkiyya suka kera.A lokacin da aka fara kaddamar da wannan aikin, wasu matsalolin suka dinka gittowa.Amma duk da haka, aka ci gaba da gudanar aiyukan kere-keren.Firaministan kasar Turkiyya na wancan zamanin, Recep Tayyip Erdoğan na da masaniya kan aiyukan da masan’antar kera kayayyakin yaki ta Santambul.Abinda yasa ya dinka karfafa gwiwar kwamandojin da ke jagorantar wannan aikin,inda ya ce “Ku ci gaba da gudanar da abinda ya dace, ina goyon bayanku dari bisa dari”.Wannan kalami da kuma dukannin tallafin da aka bayar ne, suka sa a yau aka kammala kera jirgin ruwan yaki na hudu.Bugu da kari, Turkiyya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya don kera wa kasar Pakistan jiragen ruwan yaki 4.Turkiyya ta kammala kera jirginta na ruwa na yaki na farko TCG HEYBELİADA (F-511) a ranar 27 ga watan Satumbar shekarar 2011,na biyu TCG BÜYÜKADA (F-512) a ranar 27 ga watan Satumbar shekarar 2013,inda aka fara amfani da shi a hekwatar sojojin ruwan Turkiyya,jirgin ruwan yaki na uku, TCG BURGAZADA (F-513) an kammala kera shi a ranar 18 ga watan Yunin shekarar 2016, na hudu TCG KINALIADA (F-514) kuma, a ranar 3 ga watan Yulin shekarar 2017 inda a yanzu yake ci gaba da yawo kan tekun kasar Turkiyya. 

An kera MİLGEM a matsayin Jirgin ruwan yaki ma fi karko da nagarta.Yana iya share kwanaki 10 kan teku ba tare wata matsala ko kuma wani tallafi ba.Don bin cigaban da ake da shi a yanzu haka a fagen fasaha,sau da kafa, jirgin na da matukar sauri da kuma inganci.Bugu da kari,jirage masu saukar ungulu wadanda ke da nauyin tan 10 na iya sauka da tashi kan MİLGEM ba dare ba rana.

MİLGEM, jirgin yaki ne da ka iya tafiya karkashi  da kuma kan ruwa,jirgin sintiri ne wanda aka kera don fuskantar manya-manyan barazanoni da kuma gudanar aiyukan soja.Shi yasa ya kasance a sahun jiragen yaki mafi inganci na duniya.

MİLGEM, na da fasaloli da manhajoji da dama,wadanda suka hada da:

  1. Maganadisun tsinkayen barazanoni a sararin samaniya, kan teku da karkashinsa, mafi nagarta.
  2. Manhajojin sarrafa makamai masu linzami da rokokin rugurguza barazanonin kan teku.
  3. Manhajojin sarrafa makamai masu linzami da rokokin rugurguza barazanonin samaniya.
  4. Manhajojin hangen barazanoni karkashin teku.
  5. Na’urar latroni da hasken laser ( LİS) da RF don hango maganadisu da makaman harba rokoki na G/M.

 Wannan shi ne karo na farka da ma’aikatar kera kayayyakin yaki da kuma helkwatar sojojin ruwan Turkiyya suka kaddamar da aiyukan kera jirgin ruwan yaki mafi inganci duba da cigaban fasahar duniyarmu ta yau, ba tare da sun nemi tallafa daga ketare ba.

An kera MİLGEM a masna’antar kera kayayyakin yaki na birnin Samtanbul, tare da hannaye da kuma tallafin ma’aikatan gwamanti,manyan hafsoshi da kuma kwamandojin rundunonin sojan Turkiyya.Wannan aikin ya yi matukar kyau da inganci ta yadda a yanzu haka Turkiyya ta fara siyar da jiragen ruwan yaki ga wasu kasashen waje.

An rattaba hannu a yarjejeniyar siyar da jiragen ruwan yaki 4 ga kasar Pakistan, a ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2018,kuma Turkiyya ce za ta kera su.Wadannan jiragen wadanda farashinsu ya haura dalar Amurka biliyan 5, sun kasance ciniki mafi girma da masana’antar kera kayayyakin yaki da ta taba yi a duk tsawon tarihinta.Za a kera biyu daga cikin wadannan jiragen yakin a masana’antar kera kayayyakin aiki ta Santambul, sauran  biyun kuma, a birnin Karashi na kasar Pakistan.

A yayin da a daya gefe ta fara kera jiragenta na ruwa na yaki don biyan bukatunta na tsaro, a daya bangaren kuma tana siyar da su ga kasashen ketare.Wannan ba zai zama gundunmowar tattalin arziki kawai ba.Turkiyya za ta samu nasarori a fannoni da dama ta wannan hanyar.Labarai masu alaka